Gwamnatin Bauchi ta ce ta ƙaddamar da matakan gaggawa domin dakile yaɗuwar cutar, ciki har da ƙara sa ido kan masu fama da cutar, inganta cibiyoyin jinya da kuma samar da kayayyakin magani.
Labarin Matashin da Ya Shafe Fiye da Shekara Takwas Yana Zaune Cikin Kogon Itacen Kuka a Yobe
Wani matashi mai suna Muhammadu daga ƙauyen Gudi da ke ƙaramar hukumar Fika a jihar Yobe ya ce ya shafe kusan shekara takwas yana zaune a cikin kogon wani tsohon itacen kuka, bayan ya bar rayuwa a cikin al'ummarsa.
A wata hira da ya yi, Muhammadu ya bayyana cewa ya ɗauki wannan mataki ne domin samun kwanciyar hankali, saboda a cewarsa mutane a ƙauyensu ba sa fahimtarsa.
Ya ce Allah ya ba shi damar ganin wasu abubuwan da ka iya faruwa nan gaba ta hanyar mafarkai. Sai dai duk lokacin da ya gaya wa mutanen ƙauyen abin da ya gani, sukan ɗauke shi a matsayin mai tabin hankali.
Muhammadu ya ƙara da cewa sau da dama abubuwan da ya faɗa sun kan faru daga baya, amma duk da haka hakan bai sa mutanen ƙauyen sun canja ra'ayinsu a kansa ba.
Saboda haka, ya ce ya yanke shawarar barin zama tare da jama'a, inda ya koma cikin kogon itacen kuka, wanda ya ce a nan ne yake rayuwa tun kusan shekara takwas da suka gabata.
BBC ba ta da wata hujja mai zaman kanta da ke tabbatar da iƙirarin da Muhammadu ya yi na cewa yana hangen abubuwan da za su faru ta hanyar mafarkai.
Tinubu ya yaba wa Ɗariƙar Tijjaniyya kan irin gudunmawar da take bayarwa wajen yaɗa addinin Musulunci a duniya ya ce "har yanzu muna kewar Uban mu kuma jagora Nagari Sheikh Dahiru Bauchi"
Ya ce, la'akari da tsadar rayuwa da matsin tattalin arziki da ma'aikata ke fuskanta, duk wani albashi da bai kai N500,000 ba ba zai wadatar da bukatunsu ba.
Jam'iyyar ta ce matakin zai iya samar da gidaje sama da 228,000 ga 'yan Birtaniya, yayin da kasar ke fama da karancin gidaje da kuma dogayen jerin masu jiran samun matsuguni.
An sanya hannu kan yarjejeniyar ne a yayin taron ƙolin Makkah Al-Mukarramah Summit, wanda ya haɗa da Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdoğan, da Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif.
Yan sanda sun ce mutanen sun gudanar da aikin ne ba tare da sahalewar hukumomin da ke kula da inganci da kula da magunguna da sauran hukumomin lafiya ba, lamarin da ya jawo taruwar jama'a masu yawa daga yankin Panshekara.
Kakakin MHRA ya ce ya kamata a duba waɗannan alkaluma cikin mahallin yadda miliyoyin mutane ke amfani da magungunan GLP-1 a Birtaniya. Ya ce hukumar na ci gaba da sa ido kan amincin magungunan tare da nazarin duk sabbin bayanai.
Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da koyar da matasa sana’o’in zamani, maimakon dogaro da rabon kuɗi.