Har Naji kunya  – Tinubu ya umarci EFCC ta janye umarnin kotu na rufe asusun Gwamnatin Osun

Daga Wakiliya

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya umarci Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) da ta gaggauta komawa kotu domin janye umarnin da ya sa aka daskarar (rufe) asusun gwamnatin Jihar Osun.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Fadar Shugaban Ƙasa ta fitar ranar Alhamis, bayan EFCC ta samu umarnin kotu a ranar 5 ga Agustan 2026 na daskarar da asusun gwamnatin jihar da ke First Bank.

A cewar mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, Tinubu ya sanar da Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, wannan mataki ne ta wayar tarho.

A cikin sanarwar, Shugaba Tinubu ya ce abin da ya fi ba shi kunya ba shi ne EFCC ta aiwatar da aikinta bisa umarnin kotu ba, sai dai lokacin da aka ɗauki matakin, kasancewar saura kwanaki kaɗan a gudanar da zaɓen gwamnan jihar.

Tinubu ya ce tun bayan hawansa mulki ya ba hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa da sauran hukumomin tsaro ‘yancin gudanar da ayyukansu ba tare da tsoma bakin gwamnati ba.

Sai dai ya bayyana cewa lokaci irin wannan na gab da zaɓe na iya haifar da zargin cewa ana amfani da hukumomin tarayya wajen yin tasiri kan tsarin zaɓe.

Shugaban ƙasar ya ce saboda kare mutuncin tsarin dimokuraɗiyya da tabbatar da amincewar jama'a da sahihancin zaɓe, ya umarci EFCC ta janye umarnin kotun tare da dakatar da duk wani mataki da ta ɗauka kan gwamnatin Jihar Osun dangane da lamarin.

DA DUMI-DUMI

Duk mai goyon bayan gwamnatin Tinubu an ba shi cin hanci — Fasto Odumeje

Odumeje ya kuma zargi gwamnoni da sanatoci da kare kalaman Shugaba Tinubu cewa, "Tun kafin a haife ni akwai yunwa a Najeriya," yana mai cewa a zaɓen 2027 ne za a tantance

Jami’in FRSC ya karɓi N30,000 daga hannuna, sai kuma ya manta wayarsa a cikin motata

Jami'in FRSC ya karɓi N30,000 daga hannuna, sai kuma ya manta wayarsa a cikin motata"

Allah da ya ɗauki ran Abacha kafin zaɓe yana kallon ka – Dino Melaye ya gargadi Tinubu kan zaɓen 2027

A cewarsa, akwai abin da ya kira "ikon Allah a cikin al'amuran ɗan Adam", yana mai cewa babu wani shiri na siyasa da zai iya rinjayar nufin Allah.

Anyi wa Zenith Bank Kutse an Kwashi Bayanan Kwastomomin Bankin

Zenith Bank ta bayyana cewa bayanan da aka samu damar shiga sun haɗa da wasu adireshoshin imel (email) da kuma lambobin waya na wasu kwastomomi. Sai dai bankin ya ce har yanzu binciken yana gudana.

Abubuwa 6 da za ku iya sha kafin barci domin taimakawa wajen daidaita sikarin jini da rage haɗarin kamuwa da ciwon suga

• Ka riƙa shan isasshen ruwa. • Ka yi barci na awa 7 zuwa 9 a kullum. • Ka gama cin abinci awa 2 zuwa 3 kafin kwanciya idan zai yiwu. • Idan yunwa ta taso da dare, ka zaɓi ɗan abin ci mai gina jiki maimakon kayan zaki ko abubuwan sha masu sukari.

Kanun Labarai

Mutane da dama sun samu matsalolin idanu bayan amfani da maganin ido da aka raba kyauta a Kano

Na yi zaton zan samu waraka, amma sai matsalata ta ƙaru. Ganina ya koma kamar an rufe shi da wani farin abu," in ji shi.

Ko ɗana ne ku ka kama, kada ku tausaya masa” – Gwamna Bala ya umarci jami’an tsaro su murƙushe masu haƙar ma’adinai a Bauchi...

"Ina so ku ƙara ƙaimi wajen tattara bayanan sirri. Kada ku tausaya wa kowa. Ko da ɗana ne yake da hannu a haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba, ku ɗauki mataki a kansa," in ji gwamnan.

Ba zan sake komawa Najeriya ba ko za a ba ni kyautar sama da ƙasa’ -inji ‘Yar Najeriyar da ta rasa ‘ya’yanta biyu sakamakon...

Ta ce ba talauci ko neman kuɗi ne ya sa ta bar Najeriya ba, sai dai abubuwan baƙin ciki da ta fuskanta bayan mutuwar 'ya'yanta biyu cikin ɗan gajeren lokaci.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img