An kama manajan makabarta da mai haƙa kabari kan zargin tono gawar mamaci domin satar akwatin gawa da nufin sayarwa

‘Yan sanda sun kama manajan makabarta da mai haƙa kabari kan zargin tono gawar mamaci domin satar akwatin gawa da nufin sayarwa a Akwa Ibom

Daga Wakiliya

‘Yan sandan Jihar Akwa Ibom sun ce sun kama manajan wata makabarta da wani mai haƙa kabari bisa zargin tono gawar wani da aka binne kwanan nan domin satar akwatin gawarsa da nufin sayarwa.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, Timfon John, ta ce lamarin ya faru ne a daren ranar 3 ga Agustan 2026 da misalin ƙarfe 11:30 na dare a Makabartar Mbiokporo da ke ƙaramar hukumar Nsit-Ibom.

A cewarta, wani jami'in ƙungiyar sintiri ta sa-kai ne ya hango wasu maza biyu suna ɗauke da akwatin gawa a kan babur marar rajista, lamarin da ya sa ya tare su.

‘Yan sanda sun ce ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin, Effiong Asuquo, ya tsere, yayin da aka kama Nsikak Effiong tare da miƙa shi ga jami'an tsaro.

Bayan gudanar da bincike, ‘yan sanda sun ce Nsikak Effiong ya amsa cewa shi da abokin aikinsa sun tono sabuwar kabari, suka fitar da gawar daga cikin akwatin sannan suka sace akwatin domin sayar da shi saboda neman kuɗi.

Rundunar ta ce ta kwato akwatin gawar da kuma babur ɗin da ake zargin an yi amfani da shi wajen aikata laifin.

Binciken da aka ci gaba da yi ya kai ga kama manajan makabartar, Elijah Matthew Edet, a ranar 5 ga Agusta. A cewar ‘yan sanda, ya amsa cewa ya haɗa baki da masu haƙa kabarin, yana mai cewa wannan ne karo na farko da ya shiga irin wannan aiki.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Baba Azare, ya yi Allah wadai da abin da ya bayyana a matsayin mummunan aiki na rashin mutunta mamata da kuma cin zarafin mutuncinsu. Ya kuma ba da umarnin ci gaba da bincike domin kamo duk wanda ke da hannu a lamarin, tare da yaba wa jami'an sintiri ta sa-kai saboda taka-tsantsan da suka yi.

DA DUMI-DUMI

Labarin Matashin da Ya Shafe Fiye da Shekara Takwas Yana Zaune Cikin Kogon Itacen Kuka a Yobe

Labarin Matashin da Ya Shafe Fiye da Shekara Takwas Yana Zaune Cikin Kogon Itacen Kuka a Yobe Wani matashi mai suna Muhammadu daga ƙauyen Gudi da ke ƙaramar hukumar Fika a jihar Yobe ya ce ya shafe kusan shekara takwas yana zaune a cikin kogon wani tsohon itacen kuka, bayan ya bar rayuwa a cikin al'ummarsa. A wata hira da ya yi, Muhammadu ya bayyana cewa ya ɗauki wannan mataki ne domin samun kwanciyar hankali, saboda a cewarsa mutane a ƙauyensu ba sa fahimtarsa. Ya ce Allah ya ba shi damar ganin wasu abubuwan da ka iya faruwa nan gaba ta hanyar mafarkai. Sai dai duk lokacin da ya gaya wa mutanen ƙauyen abin da ya gani, sukan ɗauke shi a matsayin mai tabin hankali. Muhammadu ya ƙara da cewa sau da dama abubuwan da ya faɗa sun kan faru daga baya, amma duk da haka hakan bai sa mutanen ƙauyen sun canja ra'ayinsu a kansa ba. Saboda haka, ya ce ya yanke shawarar barin zama tare da jama'a, inda ya koma cikin kogon itacen kuka, wanda ya ce a nan ne yake rayuwa tun kusan shekara takwas da suka gabata. BBC ba ta da wata hujja mai zaman kanta da ke tabbatar da iƙirarin da Muhammadu ya yi na cewa yana hangen abubuwan da za su faru ta hanyar mafarkai.

Mun yi kewar Shehu: Tinubu ya yaba wa Ɗariƙar Tijjaniyya kan irin gudunmawar da take bayarwa wajen yaɗa addinin Musulunci a duniya

Tinubu ya yaba wa Ɗariƙar Tijjaniyya kan irin gudunmawar da take bayarwa wajen yaɗa addinin Musulunci a duniya ya ce "har yanzu muna kewar Uban mu kuma jagora Nagari Sheikh Dahiru Bauchi"

NLC da TUC sun buƙaci a mayar da mafi ƙarancin albashi daga 70,000 zuwa N500,000

Ya ce, la'akari da tsadar rayuwa da matsin tattalin arziki da ma'aikata ke fuskanta, duk wani albashi da bai kai N500,000 ba ba zai wadatar da bukatunsu ba.

Yan Conservative sun yi alkawarin hana ‘yan Najeriya samun gidajen gwamnati a Birtaniya idan suka lashe zaɓe

Jam'iyyar ta ce matakin zai iya samar da gidaje sama da 228,000 ga 'yan Birtaniya, yayin da kasar ke fama da karancin gidaje da kuma dogayen jerin masu jiran samun matsuguni.

Kasashen Pakistan, Saudiyya da Turkiyya sun kulla yarjejeniyar tsaro: “Hari kan ɗaya, hari ne kan duka”

An sanya hannu kan yarjejeniyar ne a yayin taron ƙolin Makkah Al-Mukarramah Summit, wanda ya haɗa da Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdoğan, da Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif.

Kanun Labarai

An kama wani mutum a Birtaniya bayan ya hau rufin asibiti sanye da kayan “Mutuwa”, yana tsorata marasa lafiya

An kama wani mutum a Birtaniya bayan ya hau rufin asibiti sanye da kayan "Mutuwa" yana tsorata Mutane

‘Yan sanda a Kano sun kama mutum shida a Cocin ECWA kan zargin raba maganin ido da ake zargin yana haddasa matsalar ido

Yan sanda sun ce mutanen sun gudanar da aikin ne ba tare da sahalewar hukumomin da ke kula da inganci da kula da magunguna da sauran hukumomin lafiya ba, lamarin da ya jawo taruwar jama'a masu yawa daga yankin Panshekara.

Ana zargin alluran rage kiba na da alaƙa da mutuwar sama da mutum 200 a Birtaniya – MHRA

Kakakin MHRA ya ce ya kamata a duba waɗannan alkaluma cikin mahallin yadda miliyoyin mutane ke amfani da magungunan GLP-1 a Birtaniya. Ya ce hukumar na ci gaba da sa ido kan amincin magungunan tare da nazarin duk sabbin bayanai.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img