Yan Conservative sun yi alkawarin hana ‘yan Najeriya samun gidajen gwamnati a Birtaniya idan suka lashe zaɓe

‘Yan Conservative sun yi alkawarin hana ‘yan Najeriya samun gidajen gwamnati a Birtaniya idan suka lashe zaɓe

Daga Wakiliya

Jam'iyyar Conservative ta Birtaniya ta sanar da cewa idan ta lashe zabe na gaba, za ta hana ‘yan kasashen waje, ciki har da ‘yan Najeriya, samun sabbin gidajen gwamnati (social housing) a Ingila.

A karkashin sabon shirin, ‘yan kasashen waje ba za su sake cancantar samun sabbin gidajen gwamnati ba. Haka kuma, wasu daga cikin wadanda ke zaune a irin wadannan gidaje a yanzu za a iya ba su wa'adin watanni shida su bar gidajen.

Jam'iyyar ta ce matakin zai iya samar da gidaje sama da 228,000 ga ‘yan Birtaniya, yayin da kasar ke fama da karancin gidaje da kuma dogayen jerin masu jiran samun matsuguni.

Conservative ta zargi gwamnatin Labour da gaza shawo kan matsalar shige da fice, tana mai cewa hakan ya sa iyalan ‘yan Birtaniya ke dade suna jiran samun gidajen gwamnati.

Sai dai jam'iyyar Labour ta yi watsi da shirin, tana mai cewa ba zai yi aiki ba kuma ba zai magance matsalar gidaje da Ingila ke fuskanta ba. Ta kuma ce shirin ya yi kama da manufofin jam'iyyar Reform UK.

A karkashin shirin, mutanen da ba ‘yan Birtaniya, Ireland ko Tarayyar Turai (EU) ba za su iya rasa damar ci gaba da zama a gidajen gwamnati, har da wasu masu yara.

Sai dai ‘yan EU da ke da izinin zama na dindindin (settled status) ba za su fuskanci korar gidajensu ba.

A halin yanzu, dokokin Birtaniya na bai wa wasu ‘yan kasashen waje masu izinin zama na dindindin, ‘yan gudun hijira da masu kariyar jin kai damar neman gidajen gwamnati, yayin da masu neman mafaka ba sa cancanta sai a wasu yanayi na musamman.

Wannan ba shi ne karo na farko da jam'iyyar Conservative ke gabatar da irin wannan ra'ayi ba. A shekarar 2024, lokacin da take mulki, ta taba yin nazarin dokar da za ta tilasta wa ‘yan kasashen waje zama a Birtaniya na akalla shekaru 10 kafin su cancanci samun gidajen gwamnati.

DA DUMI-DUMI

Labarin Matashin da Ya Shafe Fiye da Shekara Takwas Yana Zaune Cikin Kogon Itacen Kuka a Yobe

Labarin Matashin da Ya Shafe Fiye da Shekara Takwas Yana Zaune Cikin Kogon Itacen Kuka a Yobe Wani matashi mai suna Muhammadu daga ƙauyen Gudi da ke ƙaramar hukumar Fika a jihar Yobe ya ce ya shafe kusan shekara takwas yana zaune a cikin kogon wani tsohon itacen kuka, bayan ya bar rayuwa a cikin al'ummarsa. A wata hira da ya yi, Muhammadu ya bayyana cewa ya ɗauki wannan mataki ne domin samun kwanciyar hankali, saboda a cewarsa mutane a ƙauyensu ba sa fahimtarsa. Ya ce Allah ya ba shi damar ganin wasu abubuwan da ka iya faruwa nan gaba ta hanyar mafarkai. Sai dai duk lokacin da ya gaya wa mutanen ƙauyen abin da ya gani, sukan ɗauke shi a matsayin mai tabin hankali. Muhammadu ya ƙara da cewa sau da dama abubuwan da ya faɗa sun kan faru daga baya, amma duk da haka hakan bai sa mutanen ƙauyen sun canja ra'ayinsu a kansa ba. Saboda haka, ya ce ya yanke shawarar barin zama tare da jama'a, inda ya koma cikin kogon itacen kuka, wanda ya ce a nan ne yake rayuwa tun kusan shekara takwas da suka gabata. BBC ba ta da wata hujja mai zaman kanta da ke tabbatar da iƙirarin da Muhammadu ya yi na cewa yana hangen abubuwan da za su faru ta hanyar mafarkai.

Mun yi kewar Shehu: Tinubu ya yaba wa Ɗariƙar Tijjaniyya kan irin gudunmawar da take bayarwa wajen yaɗa addinin Musulunci a duniya

Tinubu ya yaba wa Ɗariƙar Tijjaniyya kan irin gudunmawar da take bayarwa wajen yaɗa addinin Musulunci a duniya ya ce "har yanzu muna kewar Uban mu kuma jagora Nagari Sheikh Dahiru Bauchi"

NLC da TUC sun buƙaci a mayar da mafi ƙarancin albashi daga 70,000 zuwa N500,000

Ya ce, la'akari da tsadar rayuwa da matsin tattalin arziki da ma'aikata ke fuskanta, duk wani albashi da bai kai N500,000 ba ba zai wadatar da bukatunsu ba.

Kasashen Pakistan, Saudiyya da Turkiyya sun kulla yarjejeniyar tsaro: “Hari kan ɗaya, hari ne kan duka”

An sanya hannu kan yarjejeniyar ne a yayin taron ƙolin Makkah Al-Mukarramah Summit, wanda ya haɗa da Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdoğan, da Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif.

An kama wani mutum a Birtaniya bayan ya hau rufin asibiti sanye da kayan “Mutuwa”, yana tsorata marasa lafiya

An kama wani mutum a Birtaniya bayan ya hau rufin asibiti sanye da kayan "Mutuwa" yana tsorata Mutane

Kanun Labarai

‘Yan sanda a Kano sun kama mutum shida a Cocin ECWA kan zargin raba maganin ido da ake zargin yana haddasa matsalar ido

Yan sanda sun ce mutanen sun gudanar da aikin ne ba tare da sahalewar hukumomin da ke kula da inganci da kula da magunguna da sauran hukumomin lafiya ba, lamarin da ya jawo taruwar jama'a masu yawa daga yankin Panshekara.

An kama manajan makabarta da mai haƙa kabari kan zargin tono gawar mamaci domin satar akwatin gawa da nufin sayarwa

wani jami'in ƙungiyar sintiri ta sa-kai ne ya hango wasu maza biyu suna ɗauke da akwatin gawa a kan babur marar rajista, lamarin da ya sa ya tare su.

Ana zargin alluran rage kiba na da alaƙa da mutuwar sama da mutum 200 a Birtaniya – MHRA

Kakakin MHRA ya ce ya kamata a duba waɗannan alkaluma cikin mahallin yadda miliyoyin mutane ke amfani da magungunan GLP-1 a Birtaniya. Ya ce hukumar na ci gaba da sa ido kan amincin magungunan tare da nazarin duk sabbin bayanai.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img