Rayuwa a Sambisa: Tsoffin mayakan Boko Haram sun bayyana yadda aka yaudare su - Dole ne al'umma ta yi hakuri ta karbe su, domin idan ba haka ba, akwai yiwuwar wasu su koma daji. - Hukumomi
Bankin ya ce abubuwan da suka fi shafar yadda ’yan Najeriya ke kallon hauhawar farashi sun hada da tsadar makamashi da sufuri, rashin tsaro, matsalolin ababen more rayuwa, canjin kudin musayar waje da kuma ayyukan ’yan tsaka-tsaki.
Mutumin Kano da aka kashe wa mata da ’ya’ya shida bara ya sake aure - yana cikin wadanda aka yiwa auren gata
Daga Wakiliya
Wani mutum a Kano, Malam Haruna Bashir, wanda aka kashe wa mata da ’ya’yansa shida a shekarar da ta gabata, ya sake aure, yana cikin wadanda aka yi wa auren gata da gwamnatin jihar ta shirya.
An kashe matar Malam Haruna da ’ya’yansa shida ne a harin da wasu matasa dauke da makamai suka kai gidansu da ke yankin Dorayi a Kano.
Bayan faruwar lamarin, gwamnatin Kano ta yi alkawarin samar masa da sabon gida tare da daukar nauyin sake aurensa.
A ranar Juma’a ne aka cika alkawarin, inda aka daura wa Malam Haruna aure a bikin Auren Gata da aka gudanar a fadar Sarkin Kano.
An saka sunansa cikin maza 1,500 da suka yi aure a bikin da hukumar Hisbah ta jihar ta shirya.
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne ya jagoranci daurin auren, yayin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tsaya a matsayin waliyyin amaren, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II kuma ya wakilci angwaye.
Kamfanin ya ce manufar sabon tsarin ita ce ƙarfafa masu ƙirƙirar abubuwan asali, musamman waɗanda ke kawo sabbin bayanai, ilimi, rahotanni, nishaɗi da ra'ayoyi masu ma'ana a dandalin.
Abu mafi muhimmanci shi ne a tabbatar da cewa an zaɓi AC mai daidai da girman ɗakin. Ko Inverter ce ko Non-Inverter, AC mai girma fiye da abin da ɗakin ke buƙata ba lallai ta kasance mafi inganci ba.
Amma a yau, mafi yawan wayoyin zamani suna zuwa da batir da aka kulle a cikin jikin waya. Sai dai wannan yanayin na iya fara sauyawa daga shekara mai zuwa, musamman saboda wata sabuwar dokar Tarayyar Turai.
Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da koyar da matasa sana’o’in zamani, maimakon dogaro da rabon kuɗi.