Daga Wakiliya
Labarin Matashin da Ya Shafe Fiye da Shekara Takwas Yana Zaune Cikin Kogon Itacen Kuka a Yobe
Wani matashi mai suna Muhammadu daga ƙauyen Gudi da ke ƙaramar hukumar Fika a jihar Yobe ya ce ya shafe kusan shekara takwas yana zaune a cikin kogon wani tsohon itacen kuka, bayan ya bar rayuwa a cikin al'ummarsa.
A wata hira da ya yi da North-East Reporters, Muhammadu ya bayyana cewa ya ɗauki wannan mataki ne domin samun kwanciyar hankali, saboda a cewarsa mutane a ƙauyensu ba sa fahimtarsa.
Ya ce Allah ya ba shi damar ganin wasu abubuwan da ka iya faruwa nan gaba ta hanyar mafarkai. Sai dai duk lokacin da ya gaya wa mutanen ƙauyen abin da ya gani, sukan ɗauke shi a matsayin mai tabin hankali.
Muhammadu ya ƙara da cewa sau da dama abubuwan da ya faɗa sun kan faru daga baya, amma duk da haka hakan bai sa mutanen ƙauyen sun canja ra'ayinsu a kansa ba.
Saboda haka, ya ce ya yanke shawarar barin zama tare da jama'a, inda ya koma cikin kogon itacen kuka, wanda ya ce a nan ne yake rayuwa tun kusan shekara takwas da suka gabata.




