‘Yan sanda a Kano sun kama mutum shida a Cocin ECWA kan zargin raba maganin ido da ake zargin yana haddasa matsalar ido

‘Yan sanda a Kano sun kama mutum shida a Cocin ECWA kan zargin shiga gari suna raba maganin ido da ake zargin yana haddasa matsalar ido

Daga Wakiliya

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta ce ta kama mutum shida da ake zargi da gudanar da rabon wani maganin ido da suka Æ™era tare da sayar da shi ba tare da izinin hukumomin lafiya ba.

A cikin wata sanarwa da jami'in hulÉ—a da jama'a na rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar, ya ce jami'an 52 PMF da ke Chalawa sun kama mutanen ne a ranar 4 ga Agustan 2026 a harabar cocin ECWA da ke bayan sansanin 52 PMF a Panshekara.

Sanarwar ta ce mutanen, waɗanda ake zargin suna aiki ƙarƙashin Brother Paul Legacy Foundation kuma Simon Gbaaondo mai shekara 50 daga Karu a Jihar Nasarawa ke jagoranta, na bai wa jama'a wani maganin ido da suka ƙera, wasu kyauta wasu kuma ana sayar musu da shi.

‘Yan sanda sun ce mutanen sun gudanar da aikin ne ba tare da sahalewar hukumomin da ke kula da inganci da kula da magunguna da sauran hukumomin lafiya ba, lamarin da ya jawo taruwar jama'a masu yawa daga yankin Panshekara.

Rundunar ta ce an gayyaci wanda ya ba su masauki a harabar cocin domin taimakawa bincike, yayin da aka miƙa shari'ar zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka (CID) na rundunar domin ci gaba da bincike.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya gargadi mutane da Æ™ungiyoyi da su guji gudanar da rabon magunguna ko ayyukan jinya ba tare da amincewar gwamnatin jihar, NAFDAC da sauran hukumomin lafiya masu ruwa da tsaki ba.

Ya ce irin waÉ—annan ayyuka na iya jefa lafiyar al'umma cikin haÉ—ari, musamman idan sun haddasa cunkoson jama'a, tare da buÆ™atar mazauna jihar su rika kai rahoton duk wani aikin jinya ko rabon magunguna da suke zargin ba bisa Æ™a'ida ba ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa.

DA DUMI-DUMI

Labarin Matashin da Ya Shafe Fiye da Shekara Takwas Yana Zaune Cikin Kogon Itacen Kuka a Yobe

Labarin Matashin da Ya Shafe Fiye da Shekara Takwas Yana Zaune Cikin Kogon Itacen Kuka a Yobe Wani matashi mai suna Muhammadu daga ƙauyen Gudi da ke ƙaramar hukumar Fika a jihar Yobe ya ce ya shafe kusan shekara takwas yana zaune a cikin kogon wani tsohon itacen kuka, bayan ya bar rayuwa a cikin al'ummarsa. A wata hira da ya yi, Muhammadu ya bayyana cewa ya ɗauki wannan mataki ne domin samun kwanciyar hankali, saboda a cewarsa mutane a ƙauyensu ba sa fahimtarsa. Ya ce Allah ya ba shi damar ganin wasu abubuwan da ka iya faruwa nan gaba ta hanyar mafarkai. Sai dai duk lokacin da ya gaya wa mutanen ƙauyen abin da ya gani, sukan ɗauke shi a matsayin mai tabin hankali. Muhammadu ya ƙara da cewa sau da dama abubuwan da ya faɗa sun kan faru daga baya, amma duk da haka hakan bai sa mutanen ƙauyen sun canja ra'ayinsu a kansa ba. Saboda haka, ya ce ya yanke shawarar barin zama tare da jama'a, inda ya koma cikin kogon itacen kuka, wanda ya ce a nan ne yake rayuwa tun kusan shekara takwas da suka gabata. BBC ba ta da wata hujja mai zaman kanta da ke tabbatar da iƙirarin da Muhammadu ya yi na cewa yana hangen abubuwan da za su faru ta hanyar mafarkai.

Mun yi kewar Shehu: Tinubu ya yaba wa Ɗariƙar Tijjaniyya kan irin gudunmawar da take bayarwa wajen yaɗa addinin Musulunci a duniya

Tinubu ya yaba wa Ɗariƙar Tijjaniyya kan irin gudunmawar da take bayarwa wajen yaɗa addinin Musulunci a duniya ya ce "har yanzu muna kewar Uban mu kuma jagora Nagari Sheikh Dahiru Bauchi"

NLC da TUC sun buƙaci a mayar da mafi ƙarancin albashi daga 70,000 zuwa N500,000

Ya ce, la'akari da tsadar rayuwa da matsin tattalin arziki da ma'aikata ke fuskanta, duk wani albashi da bai kai N500,000 ba ba zai wadatar da bukatunsu ba.

Yan Conservative sun yi alkawarin hana ‘yan Najeriya samun gidajen gwamnati a Birtaniya idan suka lashe zaÉ“e

Jam'iyyar ta ce matakin zai iya samar da gidaje sama da 228,000 ga 'yan Birtaniya, yayin da kasar ke fama da karancin gidaje da kuma dogayen jerin masu jiran samun matsuguni.

Kasashen Pakistan, Saudiyya da Turkiyya sun kulla yarjejeniyar tsaro: “Hari kan É—aya, hari ne kan duka”

An sanya hannu kan yarjejeniyar ne a yayin taron ƙolin Makkah Al-Mukarramah Summit, wanda ya haɗa da Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdoğan, da Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif.

Kanun Labarai

An kama wani mutum a Birtaniya bayan ya hau rufin asibiti sanye da kayan “Mutuwa”, yana tsorata marasa lafiya

An kama wani mutum a Birtaniya bayan ya hau rufin asibiti sanye da kayan "Mutuwa" yana tsorata Mutane

An kama manajan makabarta da mai haƙa kabari kan zargin tono gawar mamaci domin satar akwatin gawa da nufin sayarwa

wani jami'in ƙungiyar sintiri ta sa-kai ne ya hango wasu maza biyu suna ɗauke da akwatin gawa a kan babur marar rajista, lamarin da ya sa ya tare su.

Ana zargin alluran rage kiba na da alaÆ™a da mutuwar sama da mutum 200 a Birtaniya – MHRA

Kakakin MHRA ya ce ya kamata a duba waÉ—annan alkaluma cikin mahallin yadda miliyoyin mutane ke amfani da magungunan GLP-1 a Birtaniya. Ya ce hukumar na ci gaba da sa ido kan amincin magungunan tare da nazarin duk sabbin bayanai.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img