Daga Wakiliya
Kasashen Pakistan da Saudiyya da kuma Turkiyya sun rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniyar tsaro ta bai ɗaya, wadda ta tanadi cewa duk wani hari da aka kai wa ɗaya daga cikin ƙasashen uku za su ɗauke shi a matsayin hari kan sauran ƙasashen biyu ( za su maida martanin taron dangi)
An sanya hannu kan yarjejeniyar ne a yayin taron ƙolin Makkah Al-Mukarramah Summit, wanda ya haɗa da Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdoğan, da Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif.
A cewar bayanan da aka fitar bayan taron, yarjejeniyar na da manufar ƙarfafa haɗin gwiwa a fannin tsaro, musayar bayanan sirri, gudanar da atisayen soji tare, da kuma bunƙasa haɗin kai wajen samar da kayan kariya da fasahar soja. Haka kuma, ta tanadi cewa idan aka kai hari kan ɗaya daga cikin ƙasashen uku, sauran za su ɗauke shi a matsayin hari a kansu.
Masu sa ido kan harkokin siyasa da tsaro sun bayyana wannan mataki a matsayin wani muhimmin sauyi a siyasar yankin Gabas ta Tsakiya, musamman a lokacin da ake fama da tashin hankali a yankin. Sai dai shugabannin ƙasashen uku sun jaddada cewa yarjejeniyar ta kare kai ce kawai, ba ta nufi wata ƙasa ko ƙungiya ta musamman ba.
Yarjejeniyar ta kuma ginu ne kan dangantakar tsaro da ta daɗe tsakanin Saudiyya da Pakistan, inda yanzu aka faɗaɗa haɗin gwiwar tare da shigar da Turkiyya cikin tsarin tsaron na bai ɗaya.





