Bauchi ta ayyana ɓarkewar cutar kwalara bayan mutuwar mutane 16
Daga Wakiliya
Gwamnatin Jihar Bauchi ta ayyana ɓarkewar cutar kwalara, bayan da aka samu tabbacin kamuwa da cutar tare da samun karuwar masu fama da gudawa mai tsanani a sassan jihar.
Kwamishinan Lafiya da Jinƙai na Jihar Bauchi, Dr Sani Mohammed Dambam, ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da aka fitar ranar 1 ga Agusta 2026.
Gwamnatin ta ce ya zuwa ranar 31 ga Yuli, an samu mutane 398 da ake zargin sun kamu da kwalara, yayin da mutane 16 suka mutu a ƙananan hukumomi 13 na jihar.
Ƙaramar Hukumar Toro ce ta fi samun yawan waɗanda ake zargin sun kamu, inda aka samu mutane 231, sai Alkaleri da Kirfi da mutane 46 kowacce, sannan Ganjuwa mai 21.
A ƙananan hukumomin Bauchi da Tafawa Balewa kuma, an samu mutane 14 a kowacce.
Dr Sani Mohammed Dambam ya ce an tabbatar da mutane shida sun kamu da nau'in kwalara mai suna Vibrio cholerae O1 Ogawa ta hanyar gwajin PCR.
Ya ce sakamakon gwajin ya tabbatar da cewa cutar na yaɗuwa a jihar, kuma yawan masu kamuwa da cutar ya cika ƙa'idojin da hukumomin lafiya na duniya da na Najeriya suka gindaya kafin ayyana ɓarkewar cutar.
Gwamnatin Bauchi ta ce ta ƙaddamar da matakan gaggawa domin dakile yaɗuwar cutar, ciki har da ƙara sa ido kan masu fama da cutar, inganta cibiyoyin jinya da kuma samar da kayayyakin magani.
An kuma tura ƙungiyoyin ma'aikatan lafiya zuwa ƙananan hukumomin da cutar ta fi shafa, yayin da gwamnati ke ƙarfafa ayyukan tsaftar muhalli da samar da ruwan sha mai tsafta.
Kwamishinan ya yi kira ga hukumomin agaji, abokan hulɗar gwamnati da masu bayar da tallafi da su taimaka da kuɗaɗe da ƙwarewa domin dakile cutar da hana ta yaɗuwa zuwa wasu sassan jihar.





