Tinubu ya karɓi jagororin Tijjaniyya, ya ce: “Har yanzu muna kewar mahaifinmu Sheikh Dahiru Bauchi”
Daga Wakiliya
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya karɓi baƙuncin tawagar Majalisar Koli ta Ɗariƙar Tijjaniyya ta duniya a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda suka kai masa ziyarar ta'aziyya kan rasuwar marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
A cikin wata sanarwa da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama'a, Sunday Dare, ya fitar, ya ce tawagar ta ƙunshi mambobi daga Aljeriya, Najeriya da Senegal, tare da wakilan Gidauniyar Sheikh Dahiru Bauchi ƙarƙashin jagorancin Khalifa-Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Sanarwar ta ce Khalifan Tijjaniyya na Aljeriya, Sheikh Ali Bin Arabi, ne ya gabatar da saƙon ta'aziyyar ga Shugaba Tinubu. Ya kuma jaddada dangantakar addini, zamantakewa da tattalin arziki da ke tsakanin Najeriya da Aljeriya, yana mai addu'ar dorewar alaƙar ruhaniya tsakanin ƙasashen biyu, tare da yi wa Najeriya da Shugaba Tinubu addu'ar zaman lafiya da ƙoshin lafiya.
Da yake mayar da martani, Shugaba Tinubu ya gode wa tawagar bisa ziyarar ta'aziyyar da suka kai masa.
Ya ce, “Har yanzu muna kewar mahaifinmu, Sheikh Dahiru Bauchi. Ya kasance uba abin ƙauna kuma jagora nagari.”
Shugaban ƙasar ya kuma yaba wa Ɗariƙar Tijjaniyya kan irin gudunmawar da take bayarwa wajen yaɗa addinin Musulunci a Afirka da sauran sassan duniya.
Marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya rasu ne a ranar 26 ga Nuwamban 2025 yana da shekara 98 a duniya.





