Musa Aliyu ya ce hukumar za ta kara amfani da fasaha da bayanai wajen dakile cin hanci da kare dukiyar gwamnati, tare da mayar da hankali kan hana barna kafin faruwar ta.
“Na karbi dukkan nauyin da ya shafi abin da ya faru a baya. Nauyin da ke kaina yanzu shi ne gyara tattalin arziki domin amfanin mafi yawan ‘yan Najeriya,” in ji shugaban.
Ya ce ya ɗauki matakin ne sakamakon abin da ya kira rashin cika alkawura daga jam’iyyar, yana mai cewa yanzu zai mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya a zaɓen 2027 a ƙarƙashin APC.
Soo a wani dogon bidiyo ta bayyana cewa dalilin da ya sa ta fara cin abinci marar nama ba wai kawai saboda kare dabbobi ko muhalli ba ne. Ta bayyana cewa tsawon shekaru tana kokarin rage kiba, kuma daga bisani tsarin vegan ya koma wani nau'in takura wa kanta wajen cin abinci saboda yadda take kallon jikinta.
Abin da Rarara ya yi wa Pantami ‘Somin taɓi ne’ ai da zarar ka bar wa’azin addini ka shiga siyasa, bai kamata ka sa ran ’yan siyasa za su ci gaba da kallonka a matsayin malamin addini ba,” in ji Rabiu Kwankwaso
Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da koyar da matasa sana’o’in zamani, maimakon dogaro da rabon kuɗi.