Matatun man fetur din mu za su dawo aiki – Tinubu
Daga Wakiliya
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta dawo da matatun man fetur na kasar da suka daina aiki, amma ya jaddada cewa nasarar su za ta dogara ne kan samar da riba da inganci, ba wai kawai ganin hayaki ko wuta daga matatar ba.
Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Najeriya (NUPENG), karkashin jagorancin shugaban kungiyar, Salimon Oladiti, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Ya ce ana sake tsara harkokin tattalin arzikin Najeriya ne domin tabbatar da cewa matatun man fetur sun dawo suna aiki yadda ya kamata.
“Matatun da kuka ambata za su dawo aiki. Amma ganin wuta da hayaki daga matata ba yana nufin tana aiki ba, sai idan tana samar da riba da kuma amfanin da aka gina ta domin samarwa,” in ji Tinubu.
Shugaban ya kuma bukaci masu motocin haya da manyan motoci da suka koma amfani da iskar gas (CNG) da su rika rage kudin sufuri ga jama’a, maimakon su rike dukkan ribar da suka samu daga saukin man fetur.
Tinubu ya ce sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatinsa ta yi sun taimaka wajen samun kudaden gudanar da manyan ayyukan hanyoyi, ciki har da hanyoyin Legas zuwa Ibadan, Abuja zuwa Kaduna da Abuja zuwa Kano.
Ya kuma sake jaddada cewa ba za a dawo da tallafin man fetur ba, yana mai cewa ya riga ya amince da alhakin gyara matsalolin tattalin arzikin da ya gada.
“Na karbi dukkan nauyin da ya shafi abin da ya faru a baya. Nauyin da ke kaina yanzu shi ne gyara tattalin arziki domin amfanin mafi yawan ‘yan Najeriya,” in ji shugaban.
Bola Tinubu ya bukaci ma’aikatan man fetur da sauran ‘yan Najeriya su ci gaba da hakuri da kuma bai wa gwamnati hadin kai, yana mai cewa gyaran tattalin arziki na bukatar lokaci da jajircewa kafin a ga cikakken sakamako.





