Daga Wakiliya
Mataimakin Dan Takarar Shugaban Kasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, kan harkokin yada labarai, Paul Ibe, ya ce zuwa yanzu tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shafe kwanaki 178 a tsare.
Paul Ibe ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya wallafa a shafin X, inda ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da amfani da shari’a wajen gallaza wa El-Rufai bayan ya sauya matsaya ta siyasa.
Ya ce El-Rufai, wanda yanzu yake cikin jam’iyyar ADC, na fuskantar abin da ya kira takura ta siyasa saboda ya raba gari da Shugaba Tinubu, duk da cewa ya goyi bayan takarar Tinubu a zaben shugaban kasa na 2023.
Ibe ya kuma yi zargin akwai bambanci wajen yadda ake tafiyar da wasu shari’o’in siyasa, inda ya ambaci batun Sanata Francis Fadahunsi da wasu tsoffin gwamnoni da ake tuhuma da laifukan rashawa.
A cewarsa, wasu ‘yan siyasa da ke fuskantar zarge-zargen cin hanci da rashawa na ci gaba da gudanar da harkokinsu cikin walwala, yayin da El-Rufai ke tsare.
Ya ce, “Wace irin shaida ake bukata don tabbatar da cewa ana yakar ‘yan adawa ne ba cin hanci da rashawa ba?”
Wannan ba shi ne karo na farko da Paul Ibe ke magana kan tsawon lokacin da El-Rufai ya shafe a tsare ba. A baya ya bayyana cewa tsohon gwamnan ya shafe kwanaki 144 da kuma kwanaki 126 a tsare, yana zargin cewa ana amfani da shari’ar wajen matsa masa lamba.
El-Rufai na fuskantar shari’o’i daban-daban da suka hada da tuhumar da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ta gabatar kan zargin almundahana da kudaden jama’a, da kuma shari’ar da ake yi masa kan zargin laifukan yanar gizo da sauraren waya ba bisa ka’ida ba.
Tsohon gwamnan Kaduna ya kasance a tsare ne tun ranar 18 ga watan Fabrairu.




