Rahoton ya ce Trump ya fito fili ya hau Air Force One, amma daga baya aka fitar da shi a asirce ta hanyar wata motar ɗaukar kayan abinci, aka kai shi wani ƙaramin jirgin soji kirar C-32A.
Hukumar ta ce ta kalli bidiyon cikin "tsananin damuwa", tana mai cewa Sheikh Jingir ya yi kira ga tsarin siyasa da ya keɓe wasu mutane bisa addininsu, sannan ya yi amfani da kalmar "kafirai" yayin da yake kira ga magoya bayansa su mallaki katin zaɓe domin "nuna musu iyakarsu".
Dr Ahmad Gumi ya ƙara da cewa ko ɓangaren adawa ma bai kamata su rika amfani da addini ba wajen harkokin siyasa inda ya wallafa bidiyon Peter Obi dan takarar Jam'iyyar NDC da aka nuna shi yana kalaman addinanci a coci.
Kalaman nasa sun zo ne a matsayin martani ga wasu kalamai da aka danganta ga Sheikh Sani Yahaya Jingir, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce musamman a kafafen sada zumunta.
G100 ta ce ta riga ta gudanar da shawarwari na sirri da wasu daga cikin manyan ‘yan siyasar adawa, ciki har da Atiku Abubakar na ADC, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso na NDC, da kuma wakilan Seyi Makinde na APM, PDP, PRP da SDP.
Haka kuma, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da duba yiwuwar kafa kwamitocin ziyara (Visitation Panels) ga jami’o’in biyu da sauran manyan makarantun jihar, domin ƙara inganta sa ido, shugabanci da yadda ake tafiyar da cibiyoyin ilimi.
Aregbesola ya bayyana hakan ne yayin wani gangamin ADC a Ejigbo, Jihar Osun, inda ya ce tsoron Allah da kuma sadaukarwarsa ga aurensa ne suka sa ya kasance mai aminci.
Shugaban kungiyar Shugabannin Makarantu ta All Nigerian Conference of Principals of Secondary Schools, Muhammad Ikililu, ya ce rashin tsaro ya dade yana kawo cikas ga tsarin makarantun kwana a jihar.
Saboda haka, suna ganin akwai buƙatar ƙarin bincike domin tabbatar da ko shan ruwan ’ya’yan itace a kai a kai na da tasiri kai tsaye wajen rage alamun damuwa.
Binciken an wallafa shi a mujallar British Journal of Nutrition, kuma Fruit Juice Science Centre ce ta ɗauki nauyin gudanar da shi.
Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da koyar da matasa sana’o’in zamani, maimakon dogaro da rabon kuɗi.