Wayoyi biyar da aka kera a China da za su iya fafatawa da Galaxy S26
Daga Wakiliya
Kamfanonin kera wayoyin salula na China na ƙara yin gogayya da manyan kamfanonin duniya, musamman a kasuwar wayoyin zamani masu tsada.
Yayin da jerin Samsung Galaxy S26 ke cikin manyan wayoyin da ake nema a kasuwar wayoyin na gani a fada (premium), wasu kamfanonin China sun ƙera wayoyin da ke da ƙarfi wajen aiki, daukar hoto, batir, caji da kuma fasahar AI.
Ga wasu daga cikin wayoyin China biyar da za su iya zama abokan hamayya ga Galaxy S26:
- Xiaomi 17 Ultra
Xiaomi 17 Ultra na daga cikin wayoyin da kamfanin ya fi mayar da hankali kan ingancin daukar hoto.
Kamfanin ya ci gaba da haɗin gwiwa da Leica wajen inganta fasahar kyamara, yayin da wayar ke kuma da na’ura mai ƙarfi, allo mai inganci da sauran kayan aikin zamani.
- Huawei Pura 80 Ultra
Huawei Pura 80 Ultra ta fi shahara wajen fasahar daukar hoto, inda kamfanin ya mayar da hankali kan inganta kyamarorin wayar.
Wayar na kuma da tsarin manhaja da tsarin na’urorin Huawei, wanda ke bambanta ta da sauran wayoyin flagship.
- Vivo X300 Pro
Vivo X300 Pro na cikin wayoyin da kamfanin Vivo ya kera domin kasuwar manyan wayoyi.
Tana da na’ura mai ƙarfi, kyamarori na zamani, allo mai inganci da kuma fasahar batir da caji.
- Oppo Find X9 Pro
Oppo Find X9 Pro na daga cikin wayoyin da ke fafatawa a kasuwar flagship.
Wayar tana da ƙirar zamani, na’ura mai ƙarfi, kyamarori na zamani da fasahar caji cikin sauri.
Oppo ta kuma ƙara mayar da hankali kan amfani da AI da fasahar sarrafa hotuna wajen inganta kwarewar masu amfani.
- Honor Magic V6
Honor Magic V6 ta bambanta da sauran wayoyin da aka ambata saboda tana da tsarin foldable, wato wayar da za a iya naɗewa.
Tana da babban allo mai lanƙwasawa, ƙirar da ba ta da kauri sosai da kuma kayan aikin da ake samu a manyan wayoyin zamani.
Wayoyin na nuna yadda kamfanonin China ke ƙara ƙalubalantar manyan kamfanoni kamar Samsung a kasuwar wayoyin salula masu inganci.




