Matar da ta shafe shekaru tana ƙaurace wa nama sai ganyayyaki ta fashe da kuka saboda santi bayan ta ci nama karo na farko
Daga Wakiliya
Wata mata mai suna Love Soo, wadda aka fi sani da Mommy Tang a shafukan sada zumunta, ta jawo hankalin jama'a bayan ta ci naman sa karo na farko cikin shekaru 14.
Soo ta shafe sama da shekaru goma tana gina suna a intanet a matsayin mai bin tsarin cin abinci na vegan, inda take wallafa bidiyoyin mukbang da girke-girken Koriya marasa nama. Tasharta ta YouTube tana da mabiya sama da 577,000.
A karshen watan Yuli ne ta sanar da cewa ta yanke shawarar barin tsarin cin ganyayyaki, bayan shekaru 14 tana binsa.
A wani bidiyo, mijinta ya dafa mata New York strip steak, inda Soo ta bayyana cewa tana cikin fargaba sosai kafin ta fara ci.
Da ta sanya nama a bakinta karo na farko, sai ta fara kuka, kafin ta ce wa mijinta: “Yana da dadi sosai.”
Ta sake cin wani yanki tare da tafarnuwa, inda ta sake fashewa da kuka tana yabon dandanon da laushin naman.
Soo a wani dogon bidiyo ta bayyana cewa dalilin da ya sa ta fara cin abinci marar nama ba wai kawai saboda kare dabbobi ko muhalli ba ne. Ta bayyana cewa tsawon shekaru tana kokarin rage kiba, kuma daga bisani tsarin vegan ya koma wani nau'in takura wa kanta wajen cin abinci saboda yadda take kallon jikinta.
Ta ce barin wannan tsarin ya sa ta ji kamar ta sauke wani nauyi da ta kwashe sama da shekaru goma tana dauke da shi.
Martanin jama'a ya kasu biyu. Wasu daga cikin tsoffin mabiyanta sun ce za su daina bibiyarta saboda komawarta cin nama, yayin da wasu suka kare ta, suna cewa batun abin da mutum zai ci da yadda yake son rayuwarsa ya rage tsakaninsa da kansa.
Soo ta ce a karshe ta zabi yin abin da take ganin zai fi dacewa da ita bayan shekaru 14 tana bin tsarin da ta saba.





