Sama da masana magunguna 9,500 suk bar Najeriya cikin shekaru biyu saboda ƙarancin albashi da kuma rashin kyawun yanayin aiki -ACPN

Sama da masana magunguna 9,500 suk bar Najeriya cikin shekaru biyu saboda ƙarancin albashi da kuma rashin kyawun yanayin aiki -ACPN

Daga Wakiliya

Ƙungiyar Masu Magunguna ta Najeriya (ACPN) ta ce sama da masana magunguna 9,500 sun bar ƙasar cikin shekaru biyu da suka gabata saboda ƙarancin albashi da kuma rashin kyawun yanayin aiki.

Ƙungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar bayan taronta na shekara-shekara karo na 45 da aka gudanar a Abuja.

ACPN ta ce “tsarin biyan albashi mara kyau”, yanayin aikin da bai gamsar ba, da kuma matsalolin rabon magunguna na daga cikin abubuwan da ke tilasta ƙwararrun ma’aikatan lafiya yin ƙaura zuwa wasu ƙasashe.

Ƙungiyar ta yi gargadin cewa ci gaba da ficewar ƙwararrun malaman magunguna na iya yin illa ga ilimin koyar da aikin pharmacy da kuma samar da ingantaccen kiwon lafiya a Najeriya.

Ta kuma bukaci gwamnatin tarayya ta haɗa kantunan magunguna na al'umma cikin tsarin kiwon lafiya na matakin farko, domin su taimaka wajen samar da magunguna masu araha da kuma kula da ƙananan cututtuka.

ACPN ta ce hakan zai rage cunkoso a asibitocin matakin sakandare da na ƙwarewa.

Ƙungiyar ta kuma yi kira da a ƙara samar da ayyukan duba lafiya a kantunan magunguna, kamar auna hawan jini da sukarin jini, ba da shawarwari kan amfani da magunguna da kuma wayar da kai kan lafiya.

A kan matsalar shaye-shayen ƙwayoyi, ACPN ta bukaci gwamnati ta ƙara tsaurara matakan gurfanar da masu safarar ƙwayoyi da masu sayar da magungunan da aka kayyade ba tare da lasisi ba.

Ta kuma bukaci Majalisar Kula da Aikin Pharmacy (PCN), NAFDAC, NDLEA da ‘yan sanda su ƙarfafa sa ido da aiwatar da dokokin da suka shafi magunguna.

ACPN ta ce akwai kuma buƙatar gyara cibiyoyin kula da masu fama da matsalar shaye-shayen ƙwayoyi da kuma ƙara samar da wasu cibiyoyi a sassan ƙasar.

Haka kuma, ƙungiyar ta yi kira ga Majalisar Dokokin Najeriya da ta kammala dokokin da suka shafi ɓangaren magunguna, ciki har da gyaran dokar Fake Drug Act.

Ta kuma ba da shawarar kafa wata hukuma ta tarayya da za ta kula da harkokin magunguna, musamman wajen daidaita saye da rarraba magunguna.

ACPN ta ce ya kamata a kafa Kwalejin Kwararrun Masana Magunguna ta Ƙasa domin inganta ƙarin ƙwarewa da ci gaba da koyar da fannin pharmacy a Najeriya.

DA DUMI-DUMI

Abin da Rarara ya yi wa Pantami ‘Somin taɓi ne’ a siyasa – Rabiu Kwankwaso

Abin da Rarara ya yi wa Pantami ‘Somin taɓi ne’ ai da zarar ka bar wa’azin addini ka shiga siyasa, bai kamata ka sa ran ’yan siyasa za su ci gaba da kallonka a matsayin malamin addini ba,” in ji Rabiu Kwankwaso

An sauya jirgin Trump a asirce saboda tsoron barazanar Iran

Rahoton ya ce Trump ya fito fili ya hau Air Force One, amma daga baya aka fitar da shi a asirce ta hanyar wata motar ɗaukar kayan abinci, aka kai shi wani ƙaramin jirgin soji kirar C-32A.

Muslim-Muslim: Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan Adam ta nemi a kama Sheikh Jingir

Hukumar ta ce ta kalli bidiyon cikin "tsananin damuwa", tana mai cewa Sheikh Jingir ya yi kira ga tsarin siyasa da ya keɓe wasu mutane bisa addininsu, sannan ya yi amfani da kalmar "kafirai" yayin da yake kira ga magoya bayansa su mallaki katin zaɓe domin "nuna musu iyakarsu".

Gumi ya gargadi Sheikh Jingir, amma ya ce a yi wa malamin uzuri: “Ya taso ne a Plateau, jihar da ake tsananin nuna ƙiyayya...

Dr Ahmad Gumi ya ƙara da cewa ko ɓangaren adawa ma bai kamata su rika amfani da addini ba wajen harkokin siyasa inda ya wallafa bidiyon Peter Obi dan takarar Jam'iyyar NDC da aka nuna shi yana kalaman addinanci a coci.

Muslim-Muslim: Idan Tinubu ya iya karanta Suratul Fatiha daidai, zan zaɓe shi-  MC Tagwaye ya ƙalubalanci Jingir

Kalaman nasa sun zo ne a matsayin martani ga wasu kalamai da aka danganta ga Sheikh Sani Yahaya Jingir, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce musamman a kafafen sada zumunta.

Kanun Labarai

Atiku, Obi, Kwankwaso da Makinde za su gana a Abuja domin duba yiwuwar dunƙulewa su marawa mutum ɗaya a 2027

G100 ta ce ta riga ta gudanar da shawarwari na sirri da wasu daga cikin manyan ‘yan siyasar adawa, ciki har da Atiku Abubakar na ADC, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso na NDC, da kuma wakilan Seyi Makinde na APM, PDP, PRP da SDP.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da ƙarin albashi ga ma’aikatan jami’o’in jihar Kano

Haka kuma, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da duba yiwuwar kafa kwamitocin ziyara (Visitation Panels) ga jami’o’in biyu da sauran manyan makarantun jihar, domin ƙara inganta sa ido, shugabanci da yadda ake tafiyar da cibiyoyin ilimi.

Ban taɓa cin amanar matata ba tun bayan aurenmu -Aregbesola

Aregbesola ya bayyana hakan ne yayin wani gangamin ADC a Ejigbo, Jihar Osun, inda ya ce tsoron Allah da kuma sadaukarwarsa ga aurensa ne suka sa ya kasance mai aminci.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img