Abin da Rarara ya yi wa Pantami ‘Somin taɓi ne’ a siyasa – Rabiu Kwankwaso

Abin da Rarara ya yi wa Pantami ‘Somin taɓi ne’ ai da zarar ka bar wa’azin addini ka shiga siyasa, bai kamata ka sa ran ’yan siyasa za su ci gaba da kallonka a matsayin malamin addini ba,” in ji Rabiu Kwankwaso

Daga Wakiliya

Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce kalaman da mawaki Dauda Kahutu Rarara ya yi wa tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, wani ɓangare ne na abin da mutum zai fuskanta idan ya shiga siyasa.

Rabiu Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da DCL, inda ya ce Rarara ya taɓa zagin sa da kuma wasu tsoffin gwamnonin Kano, ciki har da Ibrahim Shekarau da Abdullahi Umar Ganduje.

Ya ce su a matsayinsu na ’yan siyasa sun saba fuskantar irin waɗannan kalamai, kuma sun san yadda za su tafiyar da lamarin.

“Da zarar ka bar wa’azin addini ka shiga siyasa, bai kamata ka sa ran ’yan siyasa za su ci gaba da kallonka a matsayin malamin addini ba,” in ji Rabiu Kwankwaso.

Game da rikicin da ya kunno kai tsakanin Rarara da Pantami, Rabiu Kwankwaso ya ce shi ma Pantami ya taɓa yi masa kalaman batanci a gaban magoya bayansa.

Ya ce a lokacin ne shi ya nemi magoya bayansa su kwantar da hankalinsu, duk da cewa akwai lokacin da wasu daga cikin magoya bayansa suka yi ƙoƙarin ɗaukar mataki kan Pantami saboda kalaman da ya yi masa.

Rabiu Kwankwaso ya kuma yi tsokaci kan tarihin siyasar Pantami, yana mai cewa tsohon ministan ya taɓa sukar jam’iyyar PDP tare da kiran ta da wasu kalamai masu tsauri, amma daga baya ya shiga jam’iyyar kuma ya yi takara a ƙarƙashin tutarta.

Ya ce ya kamata a yi taka-tsantsan don kada Sheikh Sani Yahaya Jingir ya tsinci kansa cikin irin wannan yanayi na sauya matsaya bayan shiga siyasa.

Kalaman Rabiu Kwankwaso sun zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan wasu kalamai da Dauda Kahutu Rarara ya yi kan Isa Ali Ibrahim Pantami.

DA DUMI-DUMI

An sauya jirgin Trump a asirce saboda tsoron barazanar Iran

Rahoton ya ce Trump ya fito fili ya hau Air Force One, amma daga baya aka fitar da shi a asirce ta hanyar wata motar ɗaukar kayan abinci, aka kai shi wani ƙaramin jirgin soji kirar C-32A.

Muslim-Muslim: Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan Adam ta nemi a kama Sheikh Jingir

Hukumar ta ce ta kalli bidiyon cikin "tsananin damuwa", tana mai cewa Sheikh Jingir ya yi kira ga tsarin siyasa da ya keɓe wasu mutane bisa addininsu, sannan ya yi amfani da kalmar "kafirai" yayin da yake kira ga magoya bayansa su mallaki katin zaɓe domin "nuna musu iyakarsu".

Gumi ya gargadi Sheikh Jingir, amma ya ce a yi wa malamin uzuri: “Ya taso ne a Plateau, jihar da ake tsananin nuna ƙiyayya...

Dr Ahmad Gumi ya ƙara da cewa ko ɓangaren adawa ma bai kamata su rika amfani da addini ba wajen harkokin siyasa inda ya wallafa bidiyon Peter Obi dan takarar Jam'iyyar NDC da aka nuna shi yana kalaman addinanci a coci.

Muslim-Muslim: Idan Tinubu ya iya karanta Suratul Fatiha daidai, zan zaɓe shi-  MC Tagwaye ya ƙalubalanci Jingir

Kalaman nasa sun zo ne a matsayin martani ga wasu kalamai da aka danganta ga Sheikh Sani Yahaya Jingir, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce musamman a kafafen sada zumunta.

Atiku, Obi, Kwankwaso da Makinde za su gana a Abuja domin duba yiwuwar dunƙulewa su marawa mutum ɗaya a 2027

G100 ta ce ta riga ta gudanar da shawarwari na sirri da wasu daga cikin manyan ‘yan siyasar adawa, ciki har da Atiku Abubakar na ADC, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso na NDC, da kuma wakilan Seyi Makinde na APM, PDP, PRP da SDP.

Kanun Labarai

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da ƙarin albashi ga ma’aikatan jami’o’in jihar Kano

Haka kuma, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da duba yiwuwar kafa kwamitocin ziyara (Visitation Panels) ga jami’o’in biyu da sauran manyan makarantun jihar, domin ƙara inganta sa ido, shugabanci da yadda ake tafiyar da cibiyoyin ilimi.

Ban taɓa cin amanar matata ba tun bayan aurenmu -Aregbesola

Aregbesola ya bayyana hakan ne yayin wani gangamin ADC a Ejigbo, Jihar Osun, inda ya ce tsoron Allah da kuma sadaukarwarsa ga aurensa ne suka sa ya kasance mai aminci.

SOKOTO: An rufe makarantu a kananan hukumomi 20 saboda rashin tsaro

Shugaban kungiyar Shugabannin Makarantu ta All Nigerian Conference of Principals of Secondary Schools, Muhammad Ikililu, ya ce rashin tsaro ya dade yana kawo cikas ga tsarin makarantun kwana a jihar.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img