Labarai

Ana fargabar Amurka za ta iya kama Tinubu a Taron MDD (UNGA) – Amma Jakadan Najeriya ya ce babu abin fargaba

A wani ɓangare kuma, ya ce ba dole ba ne shugaban ƙasa ya halarci dukkan tarukan UNGA da kansa, domin ana iya tura mataimakin shugaban ƙasa ko ministan harkokin wajen ƙasa.

Idan lokaci ya yi, za mu sanar da ɗan takarar Shugaban Ƙasa guda da zai wakilci ƙawancen jam’iyyun adawa – Babangida Aliyu

Alhaji Babangida Aliyu ya bayyana hakan ne a Abuja yayin ƙaddamar da ofishin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APM,

Iyalin El-Rufai sun bai wa Ministan Tsaro kwana bakwai ya janye kalamansa ko su maka shi kotu

Sun bukaci Janar Musa ya janye zargin ta kafar da ya yi amfani da ita wajen bayyana shi, inda suka ce za su dauki matakin shari’a idan bai yi hakan ba cikin kwanaki bakwai.

“APC ba ta biyan magoya baya su halarci gangami” – Bashir Ahmad

Ya ce abin da jam’iyyar ke yi shi ne samar da isasshen abinci da abin sha, tare da tabbatar da cewa an kula da magoya bayanta yadda ya kamata a lokacin gangami da sauran shirye-shiryen jam’iyyar.

Kamfanin matatar Dangote ya sanya N5,250 a matsayin mafi ƙarancin kuɗin sayen hannun jari

Dangote ya ce an tsara shirin ne domin kowa ya samu damar mallakar wani kaso a matatar, ciki har da direbobi, masu girki, ma’aikata da manajoji.

“Duk namijin da bai tallafa wa matarsa wawa ne” – Gwamna Radda

Ya ce ya kamata maza su tallafa wa matansu idan suna son yin sana'a, domin hakan zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin iyali.

“Naira dubu N3,000 ta yi kaɗan – ba ma yi” -Waɗanda suka ce an ɗauke su haya a gangamin APC sun yi bore kan...

Wasu daga cikin mutanen sun ce matansu sun karbo bashi domin samun kuɗin abinci a gida, yayin da su kuma suke jiran a biya su kuɗin da aka yi musu alkawari.

Hisbah ta lashi takobin ƙara kaimi wajen yaƙi da ’yan daudu a Kano

A cewarsa, waɗanda aka kama sun ƙunshi mata 10 da maza 12, kuma wasu daga cikinsu sun amsa cewa suna gudanar da ayyukan kawalci wato “hook-up”, tare da yin amfani da miyagun ƙwayoyi.

Atiku zai soke tsarin biyan kudin wuta na Band A da B, ya dawo da tallafin wutar lantarki – Amaechi

Ya kuma danganta matsalar tsaro da matsin tattalin arzikin da ake fama da shi, yana cewa manoma da dama ba sa iya zuwa gonakinsu saboda rashin tsaro, lamarin da ya shafi samar da abinci.

Ku Soke Ni Ku Zage Ni, Kuma Ku Kwana Lafiya, Ba Mai Kama Ku Da Tsakar Dare – Tinubu

“A ƙarƙashin wannan gwamnati, za ku iya zagin Shugaban ƙasa, ku kai masa hari da kalamai, sannan ku koma ku kwanta ba tare da an kwankwasa ƙofarku da tsakar dare ba,” in ji Tinubu.
- Advertisement -spot_img

DA DUMI-DUMI

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img