Ana fargabar Amurka za ta iya kama Tinubu a Taron MDD (UNGA) – Amma Jakadan Najeriya ya ce babu abin fargaba
Daga Wakiliya
Ana ta yaɗa fargabar cewa Amurka na iya kama Shugaba Bola Ahmed Tinubu yayin halartar babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya, UNGA, a New York.
Sai dai Jakadan Najeriya na dindindin a Majalisar Ɗinkin Duniya, Amb. Jimoh Ibrahim, ya yi watsi da fargabar, yana mai cewa Najeriya ba ta samu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatin Amurka da ke nuna cewa za a kama shugaban ko takaita zirga-zirgarsa ba.
Jakadan ya ce yarjejeniyar da Amurka ta kulla da Majalisar Ɗinkin Duniya a shekarar 1947 ta tanadi kariya ga wakilan ƙasashe mambobin Majalisar Ɗinkin Duniya da iyalansu yayin tafiyarsu zuwa hedikwatar Majalisar da dawowarsu.
Ya ce wannan kariya ta shafi Shugaba Tinubu yayin halartar taron UNGA.
Ya kuma jaddada cewa zargin aikata laifi ba ya tabbatar da cewa mutum ya aikata laifin, sai an tabbatar da hakan ta hanyar shari’a.
Jakadan ya ce hukumomin Amurka na iya gayyatar mutum domin bayar da bayanai yayin bincike, amma hakan ba ya nufin an same shi da laifi.
A wani ɓangare kuma, ya ce ba dole ba ne shugaban ƙasa ya halarci dukkan tarukan UNGA da kansa, domin ana iya tura mataimakin shugaban ƙasa ko ministan harkokin wajen ƙasa.
A cewarsa, sama da kashi 60 cikin 100 na jerin masu jawabi a taron na bana sun ƙunshi mataimakan shugabannin ƙasashe da ministocin harkokin wajen ƙasashe.




