“Idan lokaci ya yi, za mu sanar da ɗan takarar Shugaban Ƙasa guda da zai wakilci ƙawancen jam’iyyun adawa” – Babangida Aliyu
Daga Wakiliya
Tsohon gwamnan Jihar Neja, Mu’azu Babangida Aliyu, ya ce ƙungiyar ’yan adawar da ke ƙoƙarin haɗa kan yan takara za ta bayyana ɗan takarar shugaban ƙasa guda ɗaya da za za a mara wa baya kafin zaɓen 2027.
Alhaji Babangida Aliyu ya bayyana hakan ne a Abuja yayin ƙaddamar da ofishin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APM, wanda aka gudanar a yau.
A yayin jawabin nasa, tsohon gwamnan ya yaba da kasancewar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, a wajen taron.
Ya kuma yi kira ga Peter Obi da ya haɗa kai da Gwamna Seyi Makinde da sauran ’yan takarar shugaban ƙasa domin kafa gagarumar jam’iyyar adawa.
Ya ce idan lokacin da ya dace ya yi, za a sanar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda da zai wakilci ƙawancen adawar.
Sai dai wannan batu ya jawo tambayoyi kan makomar ƙawancen, musamman ko ADC, PDP, NDC da APM na shirin kulla wata yarjejeniya ta siyasa domin tunkarar zaɓen 2027 da ɗan takara guda.
Kuma wa ya dace su tsayar idan suna son kayar da Tinubu na jam’iyyar APC?




