“APC ba ta biyan magoya baya su halarci gangami” – Bashir Ahmad

DA DUMI-DUMI

“APC ba ta biyan magoya baya su halarci gangami” – Kakakin Yakin Neman Zaben APC, Bashir Ahmad

Daga Wakiliya

Kakakin yaƙin neman zaɓen APC a ƙarƙashin City Boy Movement kana kuma Tsohon mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkokin kafafen sada zumunta, Bashir Ahmad, ya ce jam’iyyar APC ba ta biyan magoya bayanta kuɗi domin su halarci gangamin jam’iyyar.

Bashir ya bayyana hakan ne yayin da yake martani kan wani bidiyo dake yawo na wasu mutane da suka yi bore kan Naira dubu Uku- Uku da suka ce an basu

Ya ce bayan ya ga bidiyon da safiyar yau, maimakon ya yi gaggawar musanta abin da aka wallafa, sai ya tuntubi mutanen da ke da alhakin tattara magoya bayan jam’iyyar domin tabbatar da gaskiyar lamarin.

A cewarsa, amsoshin da ya samu daga dukkan waɗanda ya tuntuba sun yi daidai da abin da yake tsammani.

“Domin tabbatar da gaskiya, jam’iyyarmu ba ta biyan magoya baya kuɗi domin su halarci gangaminmu,” in ji Bashir Ahmad.

Ya ce abin da jam’iyyar ke yi shi ne samar da isasshen abinci da abin sha, tare da tabbatar da cewa an kula da magoya bayanta yadda ya kamata a lokacin gangami da sauran shirye-shiryen jam’iyyar.

Bashir ya ce idan wasu mutane yanzu suna ikirarin cewa an ba su kuɗi domin halartar gangamin APC, to hakan na buƙatar a binciki ainihin su da kuma alaƙarsu da jam’iyyar.

Ya yi zargin cewa mutanen na iya kasancewa ba ainihin magoya bayan APC ba ne, sai dai suna bayyana kansu a matsayin ’yan jam’iyyar saboda wasu dalilai da suka fi saninsu.

Ya ce APC za ta ci gaba da tattara magoya bayanta ta hanyar sahihan tsare-tsaren jam’iyyar da ƙarfin rassanta na ƙasa, maimakon biyan mutane kuɗi domin su halarci gangami.

Bashir ya ce jam’iyyar za ta ci gaba da dogaro da tsarin ta na ƙasa wajen samun goyon bayan jama’a.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img