Iyalin El-Rufai sun bai wa Ministan Tsaro kwana bakwai ya janye kalamansa ko su maka shi kotu
Daga Wakiliya
Iyalin tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, sun bai wa Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), wa’adin kwanaki bakwai da ya gabatar da hujjar zargin da ya yi masa ko kuma ya janye shi tare da neman afuwa.
Janar Musa ya yi zargin a shirin Politics Today na Channels Television a ranar 3 ga Satumba cewa El-Rufai ya shirya kashe-kashe a Kudancin Kaduna lokacin da yake gwamna.
A wata sanarwa da Mohammed Bello El-Rufai ya fitar a ranar Litinin, iyalan sun ce ba a gabatar da wata hujja da ke tabbatar da zargin ba.
Sun bukaci Janar Musa ya janye zargin ta kafar da ya yi amfani da ita wajen bayyana shi, inda suka ce za su dauki matakin shari’a idan bai yi hakan ba cikin kwanaki bakwai.
Nasir El-Rufai ya kasance gwamnan Kaduna daga 2015 zuwa 2023, kuma a halin yanzu yana cikin jagororin adawar ADC.




