“Naira dubu N3,000 ta yi kaɗan – ba ma yi” -Waɗanda suka ce an ɗauke su haya a gangamin APC sun yi bore kan kuɗin da aka ba su
Daga Wakiliya
Wasu mutane da aka ruwaito cewa an ɗauke su domin halartar wani taron jam’iyyar APC, sun koka kan abin da suka ce an biya su naira 3,000 kacal.
A wani bidiyoyi da ya yaɗu a kafafen sada zumunta, an ga mutanen sanye da rigunan kamfen, sun taru a tsaitsaye domin yi bore da nuna damuwarsu kan kuɗin da aka ba su.
Wasu daga cikinsu sun ce kuɗin da aka ba su bai kai kuɗin motar da suka kashe wajen zuwa wurin taron ba.
Jagoran matasan, Salisu Shuaibu, ya ce wasu daga cikinsu na cikin mawuyacin hali saboda rashin isasshen kuɗin ciyar da iyalansu.
“Ba mu da kuɗin da za mu ciyar da iyalanmu,” in ji shi.
Wasu daga cikin mutanen sun ce matansu sun karbo bashi domin samun kuɗin abinci a gida, yayin da su kuma suke jiran a biya su kuɗin da aka yi musu alkawari.
A cikin bidiyon, ana jin wasu daga cikin mutanen suna neman a biya su abin da suka kira alawus, inda suke cewa ba za su ci gaba da halartar tarukan jam’iyyar ba idan ba a biya su ba.
“Ku biya mu alawus ɗinmu ko kuma za mu bar APC, Bamayi,” in ji wasu daga cikin mutanen.
Ba a bayyana ainihin adadin kuɗin da aka yi wa kowane mahalarta alkawari ba, ko kuma wanda ya ɗauki nauyin biyan kuɗin ba ko lokacin da aka dauki bidiyo ba.
Har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, ba a samu martanin jam’iyyar APC ko wani jami’in da ya shirya taron kan zarge-zargen mutanen ba.




