Ku Soke Ni Ku Zage Ni, Kuma Ku Kwana Lafiya, Ba Mai Kama Ku Da Tsakar Dare – Tinubu
Daga Wakiliya
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce a ƙarƙashin gwamnatinsa, ’yan Najeriya na da damar su soke shi ko su zarge shi ba tare da fargabar kama su da tsakar dare ba.
Shugaban ya bayyana hakan ne a wani saƙon da Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ya isar a madadinsa yayin bikin cika shekaru 100 da kafuwar jaridar Daily Times of Nigeria a Abuja ranar Alhamis.
“A ƙarƙashin wannan gwamnati, za ku iya zagin Shugaban ƙasa, ku kai masa hari da kalamai, sannan ku koma ku kwanta ba tare da an kwankwasa ƙofarku da tsakar dare ba,” in ji Tinubu.
Shugaban ya ce gwamnatinsa ta fahimci muhimmiyar rawar da kafafen yaɗa labarai ke takawa wajen tsara makomar Najeriya, yana mai cewa za ta ci gaba da mutunta ’yancin aikin jarida kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin ƙasar ya tanada.
Gyare-gyaren tattalin arziki
Tinubu ya ce ’yancin yaɗa labarai na daga cikin abubuwan da ke cikin ajandar Renewed Hope ta gwamnatinsa.
Ya ce gyare-gyaren da gwamnatinsa ke aiwatarwa ba wai kawai an yi su ne domin sauya wasu manufofi ba, illa dai domin sauya yanayin tattalin arziki da zamantakewar Najeriya.
Ya ce manufofin sun haɗa da ƙarfafa tattalin arziki, inganta cibiyoyin gwamnati, jawo jari daga kasashen waje, inganta ababen more rayuwa da samar da damammaki ga matasa.




