Hisbah ta lashi takobin ƙara kaimi wajen yaƙi da ’yan daudu a Kano
Daga Wakiliya
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta ce za ta ƙara kaimi wajen yaƙi da ayyukan da take bayyana a matsayin rashin ɗa’a, bayan kama wasu mutane 22 da ake zargi da yin kwaikwayon halayen jinsi daban da nasu (daudu).
Mataimakin Babban Kwamandan Hukumar Hisbah, Dr Mujahid Aminuddeen, ya tabbatar da kamen, yana mai cewa an kama mutanen ne a wasu sassan birnin Kano, ciki har da Zoo Road da Court Road da kewaye.
Ya ce yawancin waɗanda aka kama sun shigo Kano ne daga wasu jihohin Najeriya.
A cewarsa, waɗanda aka kama sun ƙunshi mata 10 da maza 12, kuma wasu daga cikinsu sun amsa cewa suna gudanar da ayyukan kawalci wato “hook-up”, tare da yin amfani da miyagun ƙwayoyi.
Ya kuma jaddada cewa Hisbah ba za ta lamunci ayyukan da take ganin sun saɓa wa ɗabi’a da dokokin jihar ba, yana mai cewa hukumar za ta ƙara tsaurara matakan dakile irin waɗannan ayyuka a Kano.




