Atiku zai soke tsarin biyan kudin wuta na Band A da B, ya dawo da tallafin wutar lantarki – Amaechi

DA DUMI-DUMI

Atiku zai soke tsarin biyan kudin wuta na Band A da B, ya dawo da tallafin wutar lantarki – Amaechi

Daga Wakiliya

Tsohon gwamnan jihar Rivers kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Rotimi Amaechi, ya ce idan Atiku Abubakar ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027, zai dawo da tallafin wutar lantarki tare da soke tsarin biyan kuɗin wutar lantarki na Band A da Band B.

Amaechi ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin da yake kai saƙon yaƙin neman zaɓen Atiku ga mazauna ƙananan hukumomin Omuma da ke jihar Rivers.

Ya soki tsarin kuɗin wutar lantarki da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta bullo da shi, yana mai cewa cire tallafin wutar lantarkin ya janyo tashin gwauron zabi na kuɗin lantarki.

Da yake bayar da misalin abin da ya faru da shi, Amaechi ya ce kuɗin wutar lantarkin gidansa ya tashi daga N500,000 a wata zuwa Miliyan N4m a wata.

“Kuɗin wutar gidana N500,000 ne, yanzu ina biyan N4m. Atiku ya ce idan ya zo, zan koma biyan N500,000. Babu Band A da Band B, domin gwamnati za ta tallafa wa wutar,” in ji shi

Ya kuma soki cire tallafin man fetur

Amaechi ya kuma zargi gwamnatin Tinubu da ƙara tsananta halin matsin tattalin arziki bayan cire tallafin man fetur.

Ya ce matakin ya haifar da tashin farashin sufuri da kayan abinci.

“Tun da ya cire tallafin, sufuri ya ƙaru, farashin abinci ya ƙaru – tumatir, masara, komai,” in ji Amaechi.

Ya kuma danganta matsalar tsaro da matsin tattalin arzikin da ake fama da shi, yana cewa manoma da dama ba sa iya zuwa gonakinsu saboda rashin tsaro, lamarin da ya shafi samar da abinci.

A cewarsa, Atiku zai dawo da tallafin domin rage wa ‘yan Najeriya nauyin da ake fuskanta.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img