Kamfanin matatar Dangote ya sanya N5,250 a matsayin mafi ƙarancin kuɗin sayen hannun jari

DA DUMI-DUMI

Kamfanin matatar Dangote ya sanya N5,250 a matsayin mafi ƙarancin kuɗin sayen hannun jari

Daga Wakiliya

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya ce ’yan Najeriya za su iya sayen hannun jarin matatar man Dangote da kuɗi mafi ƙarancin naira 5,250.

Ya ce masu son shiga cikin sayen hannun jarin za su iya fara da hannun jari 10, inda kowanne hannun jari za a sayar da shi kan naira 525.

Dangote ya bayyana hakan ne ranar Litinin a wajen bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar fara sayar da hannun jarin matatar a wani taro da aka gudanar a Eko Hotel and Suites da ke Victoria Island, Legas.

A cewarsa, kamfanin zai bayar da jimillar hannu biliyan 4.1, da nufin tara sama da naira tiriliyan biyu domin faɗaɗa ayyukan matatar.

“A wannan IPO, muna da niyyar tara sama da naira tiriliyan biyu, a farashin naira 525 kan kowane hannun jari, yayin da mafi ƙarancin saye zai kasance hannun jari 10 kawai,” in ji Dangote.

Ya ce za a yi amfani da kuɗin da aka tara wajen faɗaɗa matatar, tare da bai wa ɗimbin ’yan Najeriya damar zama masu hannun jari a cikin kamfanin.

Dangote ya ce an tsara shirin ne domin kowa ya samu damar mallakar wani kaso a matatar, ciki har da direbobi, masu girki, ma’aikata da manajoji.

Ya ƙara da cewa mallakar hannun jarin zai ba masu zuba jari damar gina ajiyar kuɗinsu na gaba ta hanyar mallakar kaso a kamfanin.

Dangote ya bayyana IPO ɗin a matsayin “IPO na talakawa”, yana mai cewa manufarsa ita ce faɗaɗa damar ’yan Najeriya na shiga cikin mallakar ɗaya daga cikin manyan kadarorin masana’antu a ƙasar.

Ana sa ran kuɗin da za a samu daga sayar da hannun jarin zai taimaka wajen faɗaɗa matatar tare da ƙara yawan ’yan Najeriya da za su mallaki kaso a cikinta.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img