“Duk namijin da bai tallafa wa matarsa wawa ne” – Gwamna Radda

DA DUMI-DUMI

“Duk namijin da bai tallafa wa matarsa wawa ne” – Gwamna Radda

Daga Wakiliya

Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya ce duk namijin da bai tallafa wa matarsa domin ta samu abin yi na dogaro da kai, “wawa ne”, yana mai cewa hakan na iya jefa gidansa cikin matsala.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin taron CEOs Round Table Summit and Exhibition karo na huɗu, wanda ƙungiyar Initiative of Innovative Youthpreneurs Sustainable Development ta shirya a Katsina.

Ya ce ya kamata maza su tallafa wa matansu idan suna son yin sana’a, domin hakan zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin iyali.

“Duk namijin da bai tallafa wa matarsa wawa ne. Ina rantsuwa da Allah, haka nake gaya muku. Domin yana lalata gidansa da kansa,” in ji Gwamna Radda.

Ya ƙara da cewa gwamnati na ƙoƙarin samar da yanayin da zai bai wa mata da matasa damar bunƙasa sana’o’insu.

Gwamnan ya ce samun kuɗi kaɗai ba ya wadatar da ɗan kasuwa ya samu nasara, yana mai cewa akwai buƙatar samun ƙwarewa, kasuwa da kuma jari.

“Abubuwan da ake buƙata su ne ƙwarewa, kasuwa da kuɗin gudanar da sana’a,” in ji shi.

Ya kuma ce bunƙasa harkokin kasuwanci da samar da ayyukan yi ga matasa na iya taimakawa wajen rage zaman kashe wando da wasu matsalolin da ke haifar da rashin tsaro.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img