Labarai

Tinubu ya umarci ICPC ta binciki hukumar bigin da ta yi iƙirarin tana ƙarƙashin Fadar Shugaban Ƙasa

Tinubu ya ce dole ne a kare martabar Fadar Shugaban Ƙasa da hukumomin gwamnatin tarayya daga masu amfani da jabun takardu, satar suna da kuma kwaikwayon muƙaman gwamnati, yana mai umartar a hukunta duk wanda bincike ya tabbatar da laifinsa bisa tanadin doka.

Likitoci sun ba da shawarar a kwantar da El-Rufai saboda halin lafiyarsa amma ICPC ƙi yarda -inji ADC

ADC ta bukaci ICPC ta yi wa 'yan Najeriya bayani kan dalilin da ya sa aka hana iyalan El-Rufai da likitansa samun damar ganinsa, tare da bayyana dalilin kama Farfesa Bello Abubakar.

ICPC ta kama likitan El-Rufai bisa zargin ya shammaci hukumar ya haɗa El-Rufai da Isa Ashiru a Asibitinsa

ICPC ta kuma sanar da cewa ta kama likitan El-Rufai, Farfesa Bello Abubakar, domin gudanar da bincike, tana zarginsa da bayar da bayanan karya.

Gwamnonin APC yan falle ɗaya sun yi zaman sirri a Jihar Kebbi

Ana sa ran gwamnonin za su tattauna hanyoyin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatoci, inganta shugabanci nagari, bunƙasa tattalin arziki da kuma ƙarfafa haɗin kan ƙasa.

INEC ta tsawaita rajistar masu zaɓe a Legas

INEC ta tsawaita rajistar masu zaɓe a Legas domin bai wa ƙarin mutane damar yin rajista kafin zabe

Abdulaziz Ya Kaddamar da Shirin “Gani Ya Kori Ji” Don Nuna Ayyukan Tinubu a Arewa

Ya ce duk da dimbin ayyukan raya ƙasa da aka aiwatar a Arewa, mutane da dama ba su da cikakken bayani a kansu saboda ƙarancin wayar da kai.

Na hango nasarar Tinubu ba Tabbas kuma za a samu sauyi a fadar Shugaban kasa kafin zabe -inji Fasto Primate Ayodele

Haka kuma, Primate Ayodele ya ce yankin Arewa zai nuna rashin jin daɗi ga Shugaba Tinubu kafin zaɓen 2027, yana mai cewa nasarar Shugaban Ƙasar ba ta tabbata ba sai idan ya ɗauki wasu matakai masu muhimmanci.

Bilyan 23, Gidaje 5, Otel-otel: Kotu ta ba da umarnin ƙwace ƙarin kadarorin tsohon Ministan Wuta Saleh Mamman

Tun da farko dai kotun ta same shi da laifuka 12 da suka haɗa da cin hanci da safarar kuɗaɗe har kimanin Naira biliyan 33.8,

Amurka Za Ta Sa Ido Sosai Kan Zaɓen Najeriya na 2027 kuma za mu yi doka – Riley Moore

A cewarsa, wani kudirin kasafin kuɗi da ake tattaunawa a Majalisar ya ƙunshi sharuddan da za su iya takaita wasu nau'ikan tallafin Amurka ga Najeriya, har sai gwamnatin ƙasar ta ɗauki matakai kan hare-haren da ake kai wa a wasu sassan ƙasar da kuma batun tsaro.

Sule Lamido Ya Yiwa Pantami Gori Kan Yadda A Baya Ya Rika Kiran PDP “Jam’iyyar Kafirai”

Ya ƙara da cewa daga baya Pantami ya shiga PDP bayan da bai samu tikitin takarar gwamnan APC a Jihar Gombe ba, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta
- Advertisement -spot_img

DA DUMI-DUMI

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img