Sule Lamido Ya Yiwa Pantami Gori Kan Yadda A Baya Ya Rika Kiran PDP “Jam’iyyar Kafirai”

DA DUMI-DUMI


Daga Wakiliya

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya soki tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Isa Ali Pantami, inda ya tuna masa cewa a baya ya taba kiran PDP da “jam’iyyar kafirai.”

Lamido ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi ‘yan takarar gwamna na jam’iyyar PDP daga jihohin Gombe, Bauchi, Kano, Yobe da Jigawa a gidansa da ke Bamaina, Jihar Jigawa.

A cewarsa, duk da suka da zarge-zargen da aka dade ana yi wa PDP, har ma da kiranta “jam’iyyar kafirai”, bai taɓa barin jam’iyyar ba bayan ya sauka daga mulki.

Ya kuma yi ikirarin cewa bayan zaɓen 2015, manyan jagororin APC sun nemi ya koma jam’iyyarsu, amma ya ƙi, yana mai cewa ba zai bar jam’iyyar da ta ba shi damar zama Ministan Harkokin Wajen Najeriya da kuma Gwamnan Jigawa har sau biyu ba.

Lamido ya kuma yi zargin cewa Pantami, lokacin da yake Babban Limamin Masallacin Juma’a na ATBU, ya kasance yana wa’azi tare da addu’ar Allah Ya kawo ƙarshen PDP, yana kiranta “jam’iyyar kafirai.”

Ya ƙara da cewa daga baya Pantami ya shiga PDP bayan da bai samu tikitin takarar gwamnan APC a Jihar Gombe ba, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta.

Wannan na zuwa ne yayin da harkokin siyasa da sauya sheƙar ‘yan siyasa ke ƙara zafafa gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img