Na hango nasarar Tinubu ba Tabbas kuma za a samu sauyi a fadar Shugaban kasa kafin zabe -inji Fasto Primate Ayodele

Daga Wakiliya

Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele, ya ce ya hango sauye-sauye a manyan muƙaman gwamnati kafin zaɓen 2027, inda ya yi hasashen za a samu sabon Mataimakin Shugaban Ƙasa, sabon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), sabon Shugaban Majalisar Dattawa da kuma sabon Ministan Tarayya.

Primate Ayodele ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da littafinsa na hasashe na shekara-shekara mai taken Warnings To The Nations karo na 32, a wani taron manema labarai da aka gudanar a hedkwatar cocinsa da ke Lagos.

Malamin ya kuma yi iƙirarin cewa akwai shirye-shiryen da ake yi a ɓoye domin yin maguɗin zaɓen 2027, tare da cewa wani tsohon Shugaban Ƙasa ba zai goyi bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba.

Haka kuma, Primate Ayodele ya ce yankin Arewa zai nuna rashin jin daɗi ga Shugaba Tinubu kafin zaɓen 2027, yana mai cewa nasarar Shugaban Ƙasar ba tabbas sai idan ya ɗauki wasu matakai masu muhimmanci.

Baya ga haka, ya yi hasashen cewa Gwamnan Jihar Ademola Adeleke zai lashe zaɓen gwamnan Osun mai zuwa, amma ya gargade shi da ya sa ido sosai kan yadda zaɓen zai gudana, yana zargin ana matsa wa hukumar INEC lamba kan gudanar da zaɓen.

Wakiliya ta lura cewa waɗannan kalamai hasashe ne na Primate Ayodele, kuma ba su da wata hujjar hukuma da ta tabbatar da faruwarsu.

DA DUMI-DUMI

APC Za Ta Yi Amfani da Cikakken Ƙarfinta Domin Lashe Zaɓen 2027 – Nentawe Yilwatda

APC Za Ta Yi Amfani da Cikakken Ƙarfinta Domin Lashe Zaɓen 2027 Daga Kan Shugaban Kasa Har Kansila - Nentawe Yilwatda

Tsoron Talauci Na Jefa Mutane Da Dama Cikin Matsananciyar Damuwa – Masana

Tsoron Talauci Na Jefa Mutane Da Dama Cikin Matsananciyar Damuwa – Masana

Aliko Dangote Ya Yi Wasiyyar A Ware Kashi Ɗaya Bisa Uku Na Dukiyarsa, Kimanin Naira Tiriliyan 16, Domin Ayyukan Jin Ƙai — Halima Dangote

Aliko Dangote Ya Yi Wasiyyar A Ware Kashi Ɗaya Bisa Uku Na Dukiyarsa Domin Ayyukan Jin Ƙai — Halima Dangote

Kyaftin ɗin Super Falcons, Rashidat Ajibade, sanye da dankwali da aka rubuta “JESUS”

Kyaftin ɗin Super Falcons, Rashidat Ajibade, na bayyana bangaskiyarta ga Yesu a duk inda ta je.

Har Tsawon Wane Lokaci Za a Iya Ajiye Kifi a Firiza Kafin Ya Lalace?

Yawan Lokacin da Kifi Zai Iya Ɗauka a Firiza Kafin Ya Lalace

Kanun Labarai

Wani Magidanci a Kano Ya Kashe Wani Mutum Saboda Ya Yi Zargin Yana Neman Matarsa – Kiyawa

Wani Magidanci a Kano Ya Kashe Wani Mutum Saboda Ya Yi Zargin Yana Neman Matarsa – Kiyawa

Budurwa Ta Yanke Gaban Saurayinta a Kano Bayan Ya Shaida Mata Zai Auri Wata – Rundunar Yan Sanda

Budurwa Ta Yanke Gaban Saurayinta a Kano Bayan Ya Sanar da Ita Cewa Zai Auri Wata — Rundunar 'Yan Sanda

Mata Sun Fi Maza Cika Alƙawarin Biyan Bashi – Inji Rahoton Moniepoint

Moniepoint ta ce alkaluman sun nuna cewa, duk da matsalolin da mata ke fuskanta wajen samun rance saboda buƙatar jingina ko rashin tarihin bashi, suna daga cikin rukunin masu kasuwanci da suka fi nuna amana wajen biyan bashin da suka karɓa.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img