ICPC ta kama likitan El-Rufai bisa zargin ya shammaci hukumar ya haɗa El-Rufai da Isa Ashiru a Asibitinsa

Daga Wakiliya

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya (ICPC) ta zargi tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Mallam Nasir Ahmad El-Rufai, da amfani da damar da kotu ta ba shi ta zuwa duba lafiya wajen gudanar da abin da ta ce ya sabawa manufar umarnin kotu.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce kotun jihar Kaduna ta ware ranakun 6, 7 da 8 ga Yulin 2026 domin ci gaba da sauraron shari’ar da ake yi wa El-Rufai, amma bai halarci zaman farko ba saboda ya bukaci ganin likitansa na kashin kai.

ICPC ta ce, duk da cewa ta amince da bukatar bisa umarnin kotu tare da samar da tsaro, jami’anta sun gano hotuna da wani abokin siyasar El-Rufai, Isa Ashiru Kudan, ya wallafa a Facebook, yana cewa sun gana da El-Rufai a lokacin da ake zargin yana dakin ganin likita.

Hukumar ta ce hotunan sun nuna cewa an yi amfani da ziyarar asibitin wajen gudanar da wasu ayyuka da ba su cikin abin da kotu ta amince da shi, lamarin da ta bayyana a matsayin karya umarnin kotu.

ICPC ta kuma sanar da cewa ta kama likitan El-Rufai, Farfesa Bello Abubakar, domin gudanar da bincike, tana zarginsa da bayar da bayanan karya.

Hukumar ta ce za ta sanar da kotu abin da ta kira rashin bin umarnin kotu da El-Rufai ya yi, tare da jaddada cewa za ta ci gaba da gudanar da aikinta bisa doka, kuma ba za ta amince da cin zarafin kyakkyawar niyyarta daga kowane mutum ko kungiya ba.

Har zuwa lokacin wallafa wannan labari, Mallam Nasir Ahmad El-Rufai ko lauyoyinsa ba su fitar da martani kan zargin da ICPC ta yi ba.

DA DUMI-DUMI

A Watan Yuni, Kuɗin Da Ke Hannun Jama’a Ya Ragu Da Naira Biliyan 486 A Najeriya – CBN

A Watan Yuni, Kuɗin Da Ke Hannun Jama'a Ya Ragu Da Naira Biliyan 486 A Najeriya - CBN

APC Za Ta Yi Amfani da Cikakken Ƙarfinta Domin Lashe Zaɓen 2027 – Nentawe Yilwatda

APC Za Ta Yi Amfani da Cikakken Ƙarfinta Domin Lashe Zaɓen 2027 Daga Kan Shugaban Kasa Har Kansila - Nentawe Yilwatda

Tsoron Talauci Na Jefa Mutane Da Dama Cikin Matsananciyar Damuwa – Masana

Tsoron Talauci Na Jefa Mutane Da Dama Cikin Matsananciyar Damuwa – Masana

Aliko Dangote Ya Yi Wasiyyar A Ware Kashi Ɗaya Bisa Uku Na Dukiyarsa, Kimanin Naira Tiriliyan 16, Domin Ayyukan Jin Ƙai — Halima Dangote

Aliko Dangote Ya Yi Wasiyyar A Ware Kashi Ɗaya Bisa Uku Na Dukiyarsa Domin Ayyukan Jin Ƙai — Halima Dangote

Kanun Labarai

Kyaftin ɗin Super Falcons, Rashidat Ajibade, sanye da dankwali da aka rubuta “JESUS”

Kyaftin ɗin Super Falcons, Rashidat Ajibade, na bayyana bangaskiyarta ga Yesu a duk inda ta je.

Har Tsawon Wane Lokaci Za a Iya Ajiye Kifi a Firiza Kafin Ya Lalace?

Yawan Lokacin da Kifi Zai Iya Ɗauka a Firiza Kafin Ya Lalace

Wani Magidanci a Kano Ya Kashe Wani Mutum Saboda Ya Yi Zargin Yana Neman Matarsa – Kiyawa

Wani Magidanci a Kano Ya Kashe Wani Mutum Saboda Ya Yi Zargin Yana Neman Matarsa – Kiyawa
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img