Tinubu ya umarci ICPC ta binciki hukumar bigin da ta yi iƙirarin tana ƙarƙashin Fadar Shugaban Ƙasa

Daga Wakiliya

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya umarci Independent Corrupt Practices and Other Related Offences Commission ta gudanar da cikakken bincike kan wata ƙungiya da ke kiran kanta Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC), wadda gwamnatin tarayya ta ce ba ta taɓa kafa ta ba.

A cikin sanarwar da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Talata, an ce shugaban ya ba ICPC wa’adin kwanaki 30 ta kammala binciken tare da miƙa masa rahoto.

Sanarwar ta ce wani mutum mai suna Adeniyi Adeyemi Matthew ya riƙa gabatar da kansa a matsayin Darakta Janar na PFIPC, tare da iƙirarin cewa shugaban ƙasa ne ya naɗa shi, duk da cewa babu wata doka ko amincewar gwamnati da ta kafa irin wannan hukuma.

An ce binciken zai haɗa da zargin ƙirƙirar takardun naɗi na bogi, amfani da sunan shugaban ƙasa wajen neman sahalewar hukumomi da tallafin diflomasiyya, da kuma buɗe asusun banki da sunayen wasu hukumomin gwamnati ta hanyar amfani da takardun da ake zargin na bogi ne.

Haka kuma, shugaban ya umarci ICPC ta binciki duk wani mutum ko hukuma da ake zargin ta taimaka wajen aiwatar da wannan shiri, tare da gano giɓin da ke cikin tsarin gwamnati da ya ba da damar faruwar lamarin, domin ba da shawarwarin yadda za a hana sake aukuwar irin haka.

Tinubu ya ce dole ne a kare martabar Fadar Shugaban Ƙasa da hukumomin gwamnatin tarayya daga masu amfani da jabun takardu, satar suna da kuma kwaikwayon muƙaman gwamnati, yana mai umartar a hukunta duk wanda bincike ya tabbatar da laifinsa bisa tanadin doka.

DA DUMI-DUMI

APC Za Ta Yi Amfani da Cikakken Ƙarfinta Domin Lashe Zaɓen 2027 – Nentawe Yilwatda

APC Za Ta Yi Amfani da Cikakken Ƙarfinta Domin Lashe Zaɓen 2027 Daga Kan Shugaban Kasa Har Kansila - Nentawe Yilwatda

Tsoron Talauci Na Jefa Mutane Da Dama Cikin Matsananciyar Damuwa – Masana

Tsoron Talauci Na Jefa Mutane Da Dama Cikin Matsananciyar Damuwa – Masana

Aliko Dangote Ya Yi Wasiyyar A Ware Kashi Ɗaya Bisa Uku Na Dukiyarsa, Kimanin Naira Tiriliyan 16, Domin Ayyukan Jin Ƙai — Halima Dangote

Aliko Dangote Ya Yi Wasiyyar A Ware Kashi Ɗaya Bisa Uku Na Dukiyarsa Domin Ayyukan Jin Ƙai — Halima Dangote

Kyaftin ɗin Super Falcons, Rashidat Ajibade, sanye da dankwali da aka rubuta “JESUS”

Kyaftin ɗin Super Falcons, Rashidat Ajibade, na bayyana bangaskiyarta ga Yesu a duk inda ta je.

Har Tsawon Wane Lokaci Za a Iya Ajiye Kifi a Firiza Kafin Ya Lalace?

Yawan Lokacin da Kifi Zai Iya Ɗauka a Firiza Kafin Ya Lalace

Kanun Labarai

Wani Magidanci a Kano Ya Kashe Wani Mutum Saboda Ya Yi Zargin Yana Neman Matarsa – Kiyawa

Wani Magidanci a Kano Ya Kashe Wani Mutum Saboda Ya Yi Zargin Yana Neman Matarsa – Kiyawa

Budurwa Ta Yanke Gaban Saurayinta a Kano Bayan Ya Shaida Mata Zai Auri Wata – Rundunar Yan Sanda

Budurwa Ta Yanke Gaban Saurayinta a Kano Bayan Ya Sanar da Ita Cewa Zai Auri Wata — Rundunar 'Yan Sanda

Mata Sun Fi Maza Cika Alƙawarin Biyan Bashi – Inji Rahoton Moniepoint

Moniepoint ta ce alkaluman sun nuna cewa, duk da matsalolin da mata ke fuskanta wajen samun rance saboda buƙatar jingina ko rashin tarihin bashi, suna daga cikin rukunin masu kasuwanci da suka fi nuna amana wajen biyan bashin da suka karɓa.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img