Gwamnonin APC yan falle ɗaya sun yi zaman sirri a Jihar Kebbi

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Gwamnonin jihohin da aka zaɓa a ƙarƙashin jam’iyyar APC kuma suke wa’adinsu na farko sun gudanar da wani taro a ɓoye ranar Talata a Gidan Gwamnatin Jihar Kebbi da ke Birnin Kebbi.

Taron ya haɗa da gwamnonin jihohin Kaduna, Plateau, Ekiti, Delta, Zamfara, Kano, Jigawa, Ebonyi, Edo, Ondo, Kogi, Sokoto da Benue, tare da wasu ƙarin gwamnoni.

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ne ya tarbi baƙin, tare da Ministan Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Abubakar Atiku Bagudu.

Mai bai wa Gwamnan Kebbi shawara na musamman kan sabbin kafafen yaɗa labarai, Abuzaidu Yari, ya ce taron zai mayar da hankali kan muhimman batutuwan ci gaban ƙasa da kuma ajandar jam’iyyar APC.

Ana sa ran gwamnonin za su tattauna hanyoyin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatoci, inganta shugabanci nagari, bunƙasa tattalin arziki da kuma ƙarfafa haɗin kan ƙasa.

Har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, taron na ci gaba da gudana, yayin da ake sa ran Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin APC zai yi wa manema labarai bayani kan sakamakon zaman bayan kammalawarsa.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img