Daga Wakiliya
Tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, ya sake rasa wasu kadarori bayan da EFCC ta samu umarnin kotu na ƙwace su.
Mai shari’a James Omotosho na Babbar Kotun Tarayya da ke Maitama a Abuja ya bayar da umarnin ƙwace Walijam Apartments har abada, bayan kotun ta tabbatar an sayi kadarar ne da kuɗaɗen da aka samu ta haramtacciyar hanya.
Kotun ta kuma bayar da umarnin ƙwace wasu kadarori huɗu na wucin gadi, ciki har da Bloom Luxury Suites Nigeria Limited da ke Kaduna, gidaje biyu a unguwar Wuse 2 da kuma A.U.A Plaza da ke Abuja. Sai dai EFCC za ta wallafa sanarwar ƙwacen a jarida domin duk mai da’awar mallakarsu ya bayyana a gaban kotu.
Tun da farko dai kotun ta same shi da laifuka 12 da suka haɗa da cin hanci da safarar kuɗaɗe har kimanin Naira biliyan 33.8, inda aka yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekaru 75. Haka kuma kotun ta umarce shi da mayar da Naira biliyan 22 da aka gano yana da alaƙa da su.





