Abdulaziz Ya Kaddamar da Shirin “Gani Ya Kori Ji” Don Nuna Ayyukan Tinubu a Arewa

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya:

KANO – Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Harkokin Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Abdulaziz Abdulaziz, ya ƙaddamar da shirin “Gani Ya Kori Ji”, wanda zai rika kai ‘yan jarida da masu tasiri a kafafen sada zumunta ziyarar manyan ayyukan ci gaba da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta aiwatar a Arewacin Najeriya.

Abdulaziz Abdulaziz ya bayyana shirin ne a taron farko na Arewa Media Summit da aka gudanar a Kano, inda ya ce manufarsa ita ce bai wa masu yaɗa labarai damar ganin ayyukan da ido domin su isar wa jama’a sahihan bayanai.

Ya ce duk da dimbin ayyukan raya ƙasa da aka aiwatar a Arewa, mutane da dama ba su da cikakken bayani a kansu saboda ƙarancin wayar da kai.

Abdulaziz Abdulaziz ya kuma yi kira ga masu amfani da kafafen sada zumunta su rika tantance gaskiyar labarai kafin wallafawa, tare da guje wa yaɗa bayanan da za su iya haddasa rarrabuwar kawuna, musamman yayin da ake tunkarar zaɓen shekarar 2027.

Ya kuma bayyana cewa an horas da sama da masu yaɗa saƙonnin jam’iyyar APC 100 kan yadda za su isar da manufofi da ayyukan gwamnati cikin inganci da gaskiya.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img