Daga Wakiliya
Jam’iyyar ADC ta zargi Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC da kama likitan tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, tare da ikirarin cewa jami’an hukumar sun ci zarafin matarsa yayin da suka kai shi Asibitin Kasa da ke Abuja domin duba lafiyarsa.
A cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar ADC, Bolaji Abdullahi, ya fitar a ranar Talata, jam’iyyar ta ce likitocin Asibitin Kasa sun ba da shawarar a kwantar da Nasir Ahmad El-Rufai saboda halin lafiyarsa.
Sai dai ADC ta yi zargin cewa jami’an ICPC sun nace kan mayar da shi su tsare duk da shawarar da likitocin suka bayar. Jam’iyyar ta ce hakan ya haifar da takaddama tsakanin jami’an hukumar da matar El-Rufai tare da likitansa, Farfesa Bello Abubakar, inda ta yi ikirarin cewa an ci zarafin matar El-Rufai sannan aka kama likitan.
Jam’iyyar ta kuma zargi ICPC da take hakkin Nasir Ahmad El-Rufai na samun kulawar lafiya, tare da cewa hana shi ganin iyalansa, lauyoyinsa da likitansa ya saba da umarnin kotu da kuma kundin tsarin mulkin Najeriya.
ADC ta bukaci ICPC ta yi wa ‘yan Najeriya bayani kan dalilin da ya sa aka hana iyalan El-Rufai da likitansa samun damar ganinsa, tare da bayyana dalilin kama Farfesa Bello Abubakar.
Haka kuma jam’iyyar ta bukaci a bai wa Nasir Ahmad El-Rufai damar ganin iyalansa, lauyoyinsa da likitocinsa ba tare da takura ba, tare da bin dukkan ka’idojin doka wajen ci gaba da shari’arsa.
Wannan na zuwa ne bayan ICPC ta sanar da kama Farfesa Bello Abubakar, tana zarginsa da bayar da bayanan karya. Hukumar ta kuma yi zargin cewa Nasir Ahmad El-Rufai ya karya sharudan da kotu ta gindaya masa na zuwa asibiti, inda ta ce maimakon ganin likitoci, ya gudanar da ganawa da wasu abokan siyasarsa. ICPC ta ce za ta gabatar da batun gaban kotu domin daukar matakin da ya dace.





