Janar Christopher Musa ya kuma yi kira ga ’yan jam’iyyar APC da sauran ’yan Najeriya masu kishin ƙasa da su kasance cikin haɗin kai, yana mai cewa yana da yakinin APC za ta yi nasara a zaɓen 2027 tare da ci gaba da inganta shugabanci da tsaro a ƙasar.
Yari ya ce duk da kalubalen da gwamnatin Tinubu ke fuskanta, yana ganin ayyukan gwamnatin cikin shekaru uku da suka gabata za su taimaka wa APC wajen samun ƙarin wa’adi.
Ana sa ran rage kuɗin safarar man fetur zai ba ‘yan kasuwa ƙarin damar sauke farashin man a gidajen mai, idan aka samu ci gaba da rage kuɗaɗen da ke cikin tsarin rarraba man.
Daga cikin matakan da ya ba da shawara akwai sakin hatsin da ke cikin rumbunan ajiyar gwamnati zuwa wuraren da ake fama da tsananin ƙarancin abinci, da kuma ɗaukar matakan gaggawa idan ambaliyar ruwa na cikin abubuwan da ke haddasa matsalar.
A wata sanarwa da Mataimakin Sakataren Yada Labarai na Kasa na APC, Yekini Nabena, ya fitar a Abuja ranar Asabar, jam’iyyar ta bukaci Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), da Hukumar Leken Asiri kan Harkokin Kudi ta Najeriya (NFIU), da sauran hukumomi su gudanar da cikakken bincike.
Bankaɗo takardun tsofaffin laifukan da ake zargin Tinubu ko fitar da su na iya yin illa ga martabar Najeriya a idon duniya, sannan za su iya yin tasiri a zaben 2027 - Buratai ya bukaci 'yan Najeriya su yi watsi da zarge-zargen
Wasu masu fafutukar kare hakkin al'umma sun kuma ce Musulunci kansa ya yi kira da a guji barnatar da ruwa yayin alwala (almubazzaranci haramun ne a musulunci).
Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da koyar da matasa sana’o’in zamani, maimakon dogaro da rabon kuɗi.