Farashin kayayyaki na raguwa a takarda, amma a zahiri farashin abinci na ƙaruwa, talakawa na fama da matsin rayuwa – Masana
Daga Wakiliya
Wani masanin tattalin arziƙi, Farfesa Ken Ife, ya ce raguwar hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ba ta nuna cewa matsin rayuwa ya ragu ba, saboda farashin abinci na ci gaba da ƙaruwa.
Farfesa Ken Ife, wanda kuma masani ne kan manufofin gwamnati, ya bayyana hakan ne a wata hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a Abuja ranar Lahadi.
Ya yi magana ne bayan da Hukumar Kididdiga ta Ƙasa (NBS) ta fitar da rahoton hauhawar farashin kayayyaki na watan Yuli 2026.
A cewar NBS, hauhawar farashin kayayyaki gaba ɗaya ya ragu daga kashi 15.91 a watan Yuni zuwa kashi 15.43 a watan Yuli.
Sai dai hauhawar farashin abinci a kowane wata ya ƙaru sosai, daga kashi 3.75 a watan Yuni zuwa kashi 5.56 a watan Yuli.
Farfesa Ken Ife ya ce raguwar hauhawar farashin kayayyaki gaba ɗaya ta samu ne saboda raguwar farashin makamashi da kuma samun daidaito a farashin canjin kuɗin waje.
Ya ce, “Farashin makamashi ya ragu da kusan kashi 2.3, yayin da farashin canjin kuɗin waje ya samu daidaito kuma yana samun sauƙi a hankali.”
Sai dai ya ce lamarin ya bambanta a bangaren abinci, inda farashin kayan amfanin gona daga manoma ya ƙaru da kashi 4.66 a cikin wata guda.
Ya ce gaba ɗayan farashin abinci, ciki har da kayan abincin da ake shigowa da su daga ƙasashen waje, ya ƙaru da kashi 5.56 a watan Yuli.
Farfesa Ife ya danganta wannan ƙarin farashin da matsalolin jigilar kayayyaki, tsadar inshorar jiragen ruwa da kuma ƙarin farashin kayan abinci daga wuraren da ake noma su.
Ya kuma ce bambancin hauhawar farashin kayayyaki tsakanin birane da karkara na nuna irin tasirin da sufuri ke yi kan farashin abinci.
A watan Yulin, hauhawar farashin kayayyaki a birane ya kai kashi 16.12, yayin da a karkara ya tsaya kan kashi 13.77.
Masanin ya ce jihar Adamawa ce ta fi samun matsalar hauhawar farashi, inda hauhawar farashin kayayyaki gaba ɗaya ya kai kashi 33.03 a shekara, yayin da a cikin wata guda ya kai kashi 12.48.
Ya ce hauhawar farashin abinci a Adamawa ya kai kashi 51.36, wanda ya yi nisa da matsakaicin ƙasa na kashi 20.31.
Farfesa Ken Ife ya bayyana halin da ake ciki a Adamawa a matsayin “ƙararrawa”, inda ya yi kira ga hukumomi da kafafen yaɗa labarai da su binciki abubuwan da ke haddasa tsadar abinci a jihar.
Ya kuma buƙaci a ɗauki matakan gaggawa domin ƙara samar da abinci da rage wa jama’a raɗaɗin tsadar rayuwa.
Daga cikin matakan da ya ba da shawara akwai sakin hatsin da ke cikin rumbunan ajiyar gwamnati zuwa wuraren da ake fama da tsananin ƙarancin abinci, da kuma ɗaukar matakan gaggawa idan ambaliyar ruwa na cikin abubuwan da ke haddasa matsalar.




