Elektron Energy ta kuma gayyaci kamfanonin da ke Victoria Island da ke sha'awar samun wutar daga tashar da su yi rajistar nuna sha'awarsu kafin a kaddamar da aikin.
Ku rubuta wannan ku ajiye, a yau. Ni Uba Sani nake gaya muku cewa Asiwaju zai samu kashi 70 zuwa 80 cikin 100 na ƙuri'un Kaduna a 2027,” in ji gwamnan.
“Muna biyan Naira biliyan 6.7 daga bashin da muka gada, kuma za mu ci gaba da biyan sa har zuwa 2048. Tun lokacin da na zama gwamna, ban ciwo ko sisi na sabon bashi ba,” in ji Sanata Uba Sani.
Rahoton ya ce an sace mutane akalla 7,825 tsakanin watan Yulin 2025 zuwa Yunin 2026, adadin da ya karu da kashi 66 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.
Wasu ’yan Najeriya na tambayar yadda za a ce ana ƙara mayar da soyayya ta zama kasuwanci, sannan kuma a ƙayyade kuɗin shiga dandalin neman aure da daruruwan dubban naira.
Binciken jaridar The PUNCH ya nuna cewa jami’an ‘yan sandan da aka tura daga rundunar ‘yan sandan jihar Osun sun karɓi N120,000 a matsayin alawus ɗin zaɓe, wanda aka biya su ta kashi biyu na N50,000 da N70,000, kwanaki kaɗan bayan zaɓen.
Wasu jami’o’i sun zo wurina domin su gode min bayan sun shafe shekara biyu suna amfani da wutar lantarki kyauta. Na ce musu, mun gode, amma lokacin kyautar ya ƙare. Yanzu za mu zo mu ƙaddamar da tsarin, kuma za ku biya kuɗin wutar lantarki,” in ji shi.
Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da koyar da matasa sana’o’in zamani, maimakon dogaro da rabon kuɗi.