Wani babban fasto ya ƙaddamar da dandalin haɗa aure kudin shiga N700,000
Daga Wakiliya
Babban fasto kuma mai ba da shawara kan harkokin soyayya da aure, Pastor Kingsley Okonkwo, ya ƙaddamar da wani dandalin haɗa Kiristoci masu neman aure mai suna Mentor To Marry.
An ce wasu daga cikin kunshin rajistar dandalin na kai N700,000 a shekara.
Shirin na da nufin taimaka wa masu neman aure su samu abokan rayuwa masu kishin addini da kuma niyyar gina aure.
Sai dai ƙaddamar da dandalin ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, musamman kan tsadar kuɗin shiga.
Wasu ’yan Najeriya na tambayar yadda za a ce ana ƙara mayar da soyayya ta zama kasuwanci, sannan kuma a ƙayyade kuɗin shiga dandalin neman aure da daruruwan dubban naira.
Me kuke tunani kan wannan tsarin?




