Gwamnati za ta fara karɓar kuɗin wutar lantarki daga jami’o’i da asibitoci – Ministan Wuta

Lokacin shan wutar kyauta ya ƙare: Gwamnati za ta fara karɓar kuɗin wutar lantarki daga jami’o’i da asibitoci – Ministan Wuta

Daga Wakiliya

Gwamnatin Tarayya ta ce za ta fara karɓar kuɗin wutar lantarki daga jami’o’i da asibitocin koyarwa da ke amfani da cibiyoyin samar da wutar lantarki daga hasken rana da ta girka a wuraren.

Ministan Lantarki, Joseph Tegbe, ne ya bayyana hakan a Abuja yayin ƙaddamar da kamfanin kula da kadarorin makamashi mai sabuntawa na gwamnati, RAMCO.

Ministan ya ce za a sanya sabon tsarin biyan kuɗin wutar lantarki ne domin samun kuɗin kula da waɗannan kadarori da kuma tabbatar da cewa suna ci gaba da aiki.

Ya ce gwamnati ta yi nasarar gina cibiyoyi da dama, amma sau da yawa tana fuskantar matsala wajen kula da su bayan kammala su.

“Wasu jami’o’i sun zo wurina domin su gode min bayan sun shafe shekara biyu suna amfani da wutar lantarki kyauta. Na ce musu, mun gode, amma lokacin kyautar ya ƙare. Yanzu za mu zo mu ƙaddamar da tsarin, kuma za ku biya kuɗin wutar lantarki,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa irin wannan tsarin zai shafi asibitocin koyarwa da su ma ke cin gajiyar wutar lantarkin da gwamnati ta samar.

Tun daga shekarar 2017, Hukumar Samar da Wutar Lantarki a Karkara, REA, ta ce gwamnatin tarayya ta samar da megawatt 82 na wutar lantarki daga tsarin hasken rana da aka haɗa da sauran hanyoyin samar da wuta a jami’o’in gwamnatin tarayya 22 da asibitocin koyarwa uku.

Manajan Daraktan REA, Abba Aliyu, ya ce ya zama dole cibiyoyin da ke cin gajiyar waɗannan ayyuka su bayar da gudunmawa wajen kula da su ta hanyar biyan kuɗin wutar da suke amfani da ita.

Ya ce gwamnati ce ta samar da kuɗin gina kadarorin, don haka cibiyoyin da ke amfana da su ya kamata su taimaka wajen tabbatar da dorewarsu.

Daga cikin jami’o’in da ke cin gajiyar shirin akwai Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Jami’ar Najeriya da ke Nsukka da kuma Jami’ar Tarayya da ke Wukari a jihar Taraba.

Ministan Ilimi, Maruf Tunji Alausa, da Ministan Ƙananan Ma’aikatar Lafiya, Iziaq Adekunle Salako, na daga cikin manyan jami’an da suka halarci taron.

DA DUMI-DUMI

Gwamnatin Tarayya za ta sake duba tallafin karatu a ƙasashen waje

Dokta Alausa ya ce jim kaɗan bayan ya fara aiki a ma'aikatar, an gabatar masa da wani shiri da ya tanadi tura kusan ɗaliban Najeriya 100,000 zuwa Morocco domin karatun wasu darussa da ake koyarwa da Turanci, ciki har da aikin jarida da sadarwa.

Shin Muna Tunanin Za Mu Yi Watsi da Almajirai Mu Samu Zaman Lafiya?

Shin Arewa na tunanin za ta bar ’ya’yanta da mata suna yawo a kan tituna cikin talauci da rashin gata, sannan ta yi tsammanin samun zaman lafiya da ci gaba? 

Daga 1 ga Octoba WhatsApp zai fara cazar kuɗi kan saƙonnin da ake tura wa na kasuwanci

Sabon tsarin zai shafi kamfanoni da ke amfani da WhatsApp Business Platform, wadda aka fi sani da WhatsApp Business API, wajen tura saƙonni ga dimbin kwastomomi.

Dino Melaye ya shawarci Tinubu da iyalansa su fara tattara kayansu daga Villa – APC za ta sha kaye a 2027

Melaye ya ce matsalolin yunwa, kashe-kashe da sata sun nuna cewa akwai babban gibi tsakanin gwamnati da al’ummar ƙasar.

NELFUND: Mun raba wa ɗalibai miliyan 1.2 Naira biliyan 322 -Gwamnatin Tarayya 

Shugaba Tinubu ya ce ana buƙatar NELFUND ya kasance mai isasshen kuɗi kuma mai ɗorewa domin ci gaba da biyan buƙatun ɗaliban Najeriya.

Kanun Labarai

Hare-haren ’yan bindiga ya kashe mutane fiye da 10,000 cikin shekaru biyu na gwamnatin Tinubu – Amnesty

Amnesty ta ƙara da cewa ɗaruruwan ƙauyuka sun fuskanci hare-hare tare da tilasta wa mazauna barin gidajensu a jihohin Benue, Borno, Katsina, Sokoto, Plateau da Zamfara.

Gwamnatin Tinubu za ta dawo da binciken mai a Arewa bayan tsaida aikin tun bayan hawansa mulki 

Shugaban RMAFC ya kuma ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu na damuwa da yadda aikin ya tsaya, yana mai cewa an ba gwamnonin Bauchi da Gombe tabbacin cewa za a sake tura kayan aiki da ma'aikata domin ci gaba da aikin.

Duk wanda ya ce bai amfana da tallafin Tinubu ba, to baya Najeriya – Gwamnan Sokoto, Ahmed Aliyu 

Gwamnan ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su sake zaben Bola Tinubu a 2027, yana mai cewa yana da yakinin shugaban zai ci gaba da kawo sauyi a kasar.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img