‘Ba ko kaza da ta rage’ -‘yar gudun hijira ta ba da labarin ta’addancin ’yan bindiga a Zamfara
Daga Wakiliya
Wata mata mai shekara 55 da ke zaune a sansanin ’yan gudun hijira a jihar Zamfara, Fatima, ta bayyana yadda hare-haren ’yan bindiga suka tilasta mata da sauran mazauna garuruwansu barin gidajensu.
Fatima ta ce ’yan bindigar kan kewaye kauyuka domin hana mutane tserewa, inda wadanda suka yi ƙoƙarin guduwa ke fuskantar harbin bindiga, yayin da wadanda suka buya a gidaje ke fuskantar kona musu gidajen.
Ta ce wani kauye da ke kusa da nasu ya zama kufai bayan hare-haren.
“Ba ko kaza guda da ta rage a can,” in ji ta.
A wata hira da BBC a ƙarshen mako, Fatima ta ce ’yan bindigar sun kai hari garinsu da misalin ƙarfe biyu na dare, inda suka raba kansu zuwa rukuni uku.
A cewarta, rukuni na farko ya tsaya a bakin ƙauyen, na biyu ya shiga cikin ƙauyen, yayin da na uku ya tsaya a bayan garin domin hana mazauna tserewa.
“Idan ka shiga ɗaki, sai su ƙona ɗakin. Idan ka fito ka yi ƙoƙarin guduwa, sai su harbe ka,” in ji Fatima.
Ta ce ’yan bindigar kan yi ta harbe-harbe ba tare da nuna tausayi ba.
Fatima ta ce a wasu hare-haren, ’yan bindigar kan zo a ɗaruruwansu, inda ta yi kiyasin cewa ana iya ganin babura kusan 100, kuma kowane babur na ɗauke da mutum uku.
Ta ce a watan Yuni an kashe kusan mutum 70, ciki har da yara, a ƙauyen Bia Buki.
Daga cikin wadanda aka kashe, ta ce har da mijinta da ’yan’uwanta shida daga cikin bakwai.
Ta kuma ce wasu yara sun ji raunuka yayin da suke ƙoƙarin tserewa ta cikin daji, inda wasu suka faɗa cikin ramuka.
Bayan harin, Fatima ta ce ta tsere tare da wasu mazauna ƙauyen da ’ya’yansu zuwa wani daji da ke kusa, wanda suka mayar da shi mafaka.
“Dajin ya zama mafakarmu. Mun gudu da ’ya’yanmu. Idan ba ka samu ɗanka ba, sai ka ɗauki ɗan maƙwabcinka,” in ji ta.
Daga bisani, mutanen da suka rasa matsugunansu suka isa Gusau, babban birnin jihar Zamfara, inda Fatima ke zaune a wani sansanin wucin gadi tare da ’ya’yanta bakwai, wadanda shekarunsu suka kama daga tara zuwa 30.
Ta ce rayuwa a sansanin na da matuƙar wahala, saboda rashin isasshen matsuguni da abinci, yayin da tallafin da suke samu bai zuwa akai-akai ba.
“Mun kasance masu wadata lokacin da ake zaman lafiya, amma yanzu komai ya canza kuma mun zama mabarata,” in ji ta cikin kuka.
Fatima ta ce a wasu lokuta ana tura yara daga sansanin zuwa neman itacen girki domin sayarwa da samun kuɗin sayen abinci.
Sai dai ta ce ’yan bindiga sun yi garkuwa da yara 22 daga cikin wadanda ke zuwa neman itacen.
Duk da cewa sansanin da take zaune yana da nisan kusan kilomita 25 daga garinsu, Fatima ta ce har yanzu tana rayuwa cikin fargabar sake kai musu hari.
“Lokacin da na fara zuwa sansanin, karar harbe-harbe da ake ji da daddare ta hana ni barci,” in ji ta.
Sai dai ta ce yanayin tsaro ya ɗan inganta saboda yawan sintirin sojoji da ’yan banga da gwamnati ke tallafawa, ko da yake har yanzu tsoro bai gushe ba.
A cewar rahoton BBC, Fatima na daga cikin kimanin mutane 800,000 da rikicin ya raba da muhallansu a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.
Rashin tsaro da hare-haren ’yan bindiga na daga cikin manyan dalilan da suka tilasta wa dubban mutane barin gidajensu a yankin.
’Yan bindiga sun dade suna kai hare-hare a wasu sassan Arewa maso Yamma, inda ake zargin kungiyoyin masu dauke da makamai da amfani da babura wajen kai hare-hare kan kauyuka da manyan hanyoyi, kafin su tsere kafin jami’an tsaro su isa.
Ana kuma zargin ’yan bindigar da yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, satar dukiyoyi da kuma karbar haraji daga manoma kafin su ba su damar zuwa gonakinsu.
A wasu yankunan, mazauna kauyuka kan biya makudan kudade ga ’yan bindigar domin samun damar ci gaba da zama ko gudanar da harkokinsu.
