Ana dab da kammala wata sabuwar tashar samar da wutar lantarki mai karfin 40MW a Lagos
Daga Wakiliya
Ana dab da kammala wata sabuwar tashar samar da wutar lantarki mai karfin megawatt 40 da kamfanin Elektron Energy ke ginawa a tsibirin Legas.
Kamfanin ya ce tashar za ta fara aiki domin samar da wutar lantarki ga ‘yan kasuwa da kamfanonin da ke gudanar da harkokinsu a yankin Victoria Island na jihar Legas.
An bayyana hakan ne a yayin wani taron Victoria Island Power Customer Experience Day, inda aka bai wa wasu ‘yan kasuwa da shugabannin kamfanoni damar ziyartar tashar tare da samun bayani kan ci gaban aikin.
A yayin ziyarar, mahalarta sun samu bayanai kan yadda tashar za ta rika aiki, da kuma fasahar injunan Wärtsilä da ake amfani da su wajen samar da wutar.
Ana gina aikin ne tare da hadin gwiwar kamfanin rarraba wutar lantarki na Eko Electricity Distribution Company, karkashin lasisin Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Jihar Legas.
Elektron Energy ta ce tashar za ta samar da wutar lantarki na musamman kuma abin dogaro ga kamfanonin da ke Victoria Island ta hanyar wata hanyar rarraba wutar da kwararru za su rika kula da ita.
Kamfanin ya ce hakan zai bai wa ‘yan kasuwa damar rage dogaro da janaretocin diesel, tare da rage musu kudaden man fetur da gyaran janareto.
Babban Daraktan Ci gaban Kasuwanci na Elektron Energy, Ayomide Oladapo, ya ce rashin tabbas wajen samun wutar lantarki ya dade yana jefa kamfanoni a Victoria Island cikin matsala.
Ya ce kamfanoni sun kasance suna fuskantar zabin ko dai su dauki nauyin samar da wutar da kansu ta hanyar janareto, ko kuma su dogara da wutar lantarki daga wutar Najeriya (National grid) wadda ba ta da tabbas.
A cewarsa, sabon aikin zai ba kamfanonin damar samun wutar da za ta taimaka musu wajen tsara harkokinsu, kara yawan aiki da kuma bunkasa kasuwancinsu.
Shi ma Manajan Kamfanin Wärtsilä mai kula da ayyukan tashar, Mika Gummerus, ya ce aikin ya hada kwarewar fasaha, manyan ababen more rayuwa da kuma tsare-tsaren dogon lokaci domin inganta samar da wutar lantarki ga ‘yan kasuwa.
Ya ce hadin gwiwar kamfanonin na da nufin samar da wutar lantarki mai inganci da kuma rage matsalolin da kasuwanci ke fuskanta sakamakon rashin tabbas wajen samun wuta.
Rahotanni sun ce ARM-Harith Infrastructure Fund, Nigeria Sovereign Investment Authority, InfraCredit da Bank of Industry na daga cikin wadanda suka tallafa wa aikin.
Elektron Energy ta kuma gayyaci kamfanonin da ke Victoria Island da ke sha'awar samun wutar daga tashar da su yi rajistar nuna sha'awarsu kafin a kaddamar da aikin.




