Jami’an tsaron da aka tura aikin zaben Osun sun koka kan rashin biyansu alawus ɗin aikin
Daga Wakiliya
Wasu jami’an tsaro da aka tura aikin tabbatar da tsaro a zaɓen gwamnan jihar Osun na ranar 15 ga watan Agusta sun koka kan rashin biyan su alawus ɗin aikin zaɓen.
Jami’an da lamarin ya shafa sun haɗa da na Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC), Hukumar Shige da Fice (NIS), Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali (NCoS) da Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya.
Binciken jaridar The PUNCH ya nuna cewa jami’an ‘yan sandan da aka tura daga rundunar ‘yan sandan jihar Osun sun karɓi N120,000 a matsayin alawus ɗin zaɓe, wanda aka biya su ta kashi biyu na N50,000 da N70,000, kwanaki kaɗan bayan zaɓen.
Sai dai wasu daga cikin jami’an sauran hukumomin sun ce har yanzu ba a biya su kuɗin aikin ba.
NSCDC ta ce ta tura jami’ai 10,210 zuwa jihar Osun, ciki har da jami’an ɗauke da makamai daga jihohin Kudu maso Yamma da wasu jihohi da suka haɗa da Kano, Nasarawa, Kogi, Kaduna da Abuja.
Haka kuma, kimanin jami’ai 300 daga Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali, akasari daga rundunar jihar Osun, aka tura aikin zaɓen.
Wani jami’in NSCDC da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa The PUNCH cewa sun isa Osogbo ranar 10 ga Agusta, inda aka sauke su a harabar wata makarantar sakandare kafin daga bisani a kai su hedikwatar hukumar.
Ya ce a lokacin da suke can sun koka kan rashin wadataccen kulawa, inda suka nemi a ba su kuɗin ciyarwa.
A cewarsa, an ba kowanne daga cikinsu N30,000 kafin a tura su ƙananan hukumomin da aka sanya su.
Sai dai ya ce tun bayan dawowarsa sansaninsa, ba a sake biyansa wani kuɗi ba.
Ya bayyana cewa yanayin da suka yi aikin zaɓen a ciki ya kasance mai wahala, lamarin da ya ce ya sa rashin biyan alawus ɗin ya ƙara musu takaici.
NSCDC ta ce ana biyan kuɗin
Jami’in hulɗa da jama’a na NSCDC, Babawale Afolabi, ya ce jinkirin biyan kuɗin ya samo asali ne sakamakon buƙatar tantance bayanan jami’an da aka tura aikin.
Ya ce hukumar ta fara biyan kuɗin bayan kammala tantance sunayen jami’an tare da kwamandojin jihohi.
A cewarsa, jami’an da ba su karɓi kuɗinsu ba su yi haƙuri, domin za a biya duk wanda ya shiga aikin zaɓen.
Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali kuwa ta ce jami'arta mai magana da yawun hukumar, Jane Osuji, ba ta da masaniya kan ƙorafin, inda ta tura The PUNCH zuwa ga jami’in hulɗa da jama’a na rundunar Osun, Joel Oyedokun.
Sai dai ba a samu amsar kiraye-kirayen da aka yi masa ko saƙon WhatsApp da aka aika masa ba.
Haka kuma, jaridar ta ce ba ta samu damar jin ta bakin Hukumar Shige da Fice da Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya ba kan batun.




