Uba Sani ya ce Tinubu zai samu kashi 70 zuwa 80 cikin 100 na ƙuri'un Kaduna a 2027
Daga Wakiliya
Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani, ya yi hasashen cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai samu sama da kashi 70 zuwa 80 cikin 100 na ƙuri'un jihar Kaduna a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels Television.
Sanata Uba Sani ya ce yana da yaƙinin cewa al'ummar Kaduna za su marawa Shugaba Tinubu baya a zaɓen na 2027.
“Ku rubuta wannan ku ajiye, a yau. Ni Uba Sani nake gaya muku cewa Asiwaju zai samu kashi 70 zuwa 80 cikin 100 na ƙuri'un Kaduna a 2027,” in ji gwamnan.
Ya kuma bayyana kwarin gwiwarsa kan irin goyon bayan da yake ganin shugaban zai samu a jihar yayin zaɓen.



