Gwamnan Kaduna ya ce jihar na biyan N6.7bn na bashin da ta gada

Daga Wakiliya

Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani, ya ce gwamnatin jihar na biyan Naira biliyan 6.7 a matsayin bashin da ta gada, wanda ya ce za a ci gaba da biya har zuwa shekarar 2048.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata hira da shirin One-on-One na Channels Television.

Sanata Uba Sani ya ce bai cika son yawan fitowa yana surutai ba amma bashin wani bangare ne na rancen da ya gada daga gwamnatin da ta gabata, wanda ake ci gaba da biyan sa daga kudaden da jihar ke samu ta hanyar rabon kudaden tarayya na FAAC.

Ya kuma ce tun bayan da ya zama gwamnan Kaduna, bai karɓi wani sabon bashi ba.

“Muna biyan Naira biliyan 6.7 daga bashin da muka gada, kuma za mu ci gaba da biyan sa har zuwa 2048. Tun lokacin da na zama gwamna, ban ciwo ko sisi na sabon bashi ba,” in ji Sanata Uba Sani.

Gwamnan ya ce matakin na daga cikin kokarin gwamnatinsa na tabbatar da cewa jihar ba ta kara shiga wani sabon nauyin bashi ba.

DA DUMI-DUMI

Uba Sani ya ce Tinubu zai samu kashi 70 zuwa 80 cikin 100 na ƙuri’un Kaduna a 2027

Ku rubuta wannan ku ajiye, a yau. Ni Uba Sani nake gaya muku cewa Asiwaju zai samu kashi 70 zuwa 80 cikin 100 na ƙuri'un Kaduna a 2027,” in ji gwamnan.

Masu garkuwa sun karɓi kusan dala miliyan 5.8 a Najeriya – SBM Intelligence

Rahoton ya ce an sace mutane akalla 7,825 tsakanin watan Yulin 2025 zuwa Yunin 2026, adadin da ya karu da kashi 66 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.

Wani babban fasto ya ƙaddamar da dandalin haɗa aure kudin shiga N700,000

Wasu ’yan Najeriya na tambayar yadda za a ce ana ƙara mayar da soyayya ta zama kasuwanci, sannan kuma a ƙayyade kuɗin shiga dandalin neman aure da daruruwan dubban naira.

Jami’an tsaron da aka tura aikin zaben Osun sun koka kan rashin biyansu alawus ɗin aikin

Binciken jaridar The PUNCH ya nuna cewa jami’an ‘yan sandan da aka tura daga rundunar ‘yan sandan jihar Osun sun karɓi N120,000 a matsayin alawus ɗin zaɓe, wanda aka biya su ta kashi biyu na N50,000 da N70,000, kwanaki kaɗan bayan zaɓen.

Gwamnati za ta fara karɓar kuɗin wutar lantarki daga jami’o’i da asibitoci – Ministan Wuta

Wasu jami’o’i sun zo wurina domin su gode min bayan sun shafe shekara biyu suna amfani da wutar lantarki kyauta. Na ce musu, mun gode, amma lokacin kyautar ya ƙare. Yanzu za mu zo mu ƙaddamar da tsarin, kuma za ku biya kuɗin wutar lantarki,” in ji shi.

Kanun Labarai

Gwamnatin Tarayya za ta sake duba tallafin karatu a ƙasashen waje

Dokta Alausa ya ce jim kaɗan bayan ya fara aiki a ma'aikatar, an gabatar masa da wani shiri da ya tanadi tura kusan ɗaliban Najeriya 100,000 zuwa Morocco domin karatun wasu darussa da ake koyarwa da Turanci, ciki har da aikin jarida da sadarwa.

Shin Muna Tunanin Za Mu Yi Watsi da Almajirai Mu Samu Zaman Lafiya?

Shin Arewa na tunanin za ta bar ’ya’yanta da mata suna yawo a kan tituna cikin talauci da rashin gata, sannan ta yi tsammanin samun zaman lafiya da ci gaba? 

Daga 1 ga Octoba WhatsApp zai fara cazar kuɗi kan saƙonnin da ake tura wa na kasuwanci

Sabon tsarin zai shafi kamfanoni da ke amfani da WhatsApp Business Platform, wadda aka fi sani da WhatsApp Business API, wajen tura saƙonni ga dimbin kwastomomi.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img