Masu garkuwa sun karɓi kusan dala miliyan 5.8 (kimanin Naira Biliyan 8) a Najeriya – SBM Intelligence
Daga Wakiliya
Wani rahoto da cibiyar bincike kan tsaro ta SBM Intelligence ta fitar ya ce masu garkuwa da mutane a Najeriya sun karɓi kusan dala miliyan 5.8, kwatankwacin naira biliyan 7.78, a matsayin kudin fansa cikin shekara guda.
Rahoton ya ce an sace mutane akalla 7,825 tsakanin watan Yulin 2025 zuwa Yunin 2026, adadin da ya karu da kashi 66 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.
SBM ta kuma ce aƙalla mutane 1,142 aka kashe cikin wannan lokaci.
Cibiyar ta tattara alkaluman ne daga rahotannin kafafen yaɗa labarai, hirarraki da kuma bayanan da ke a fili. Ta ce adadin kudin fansar da aka tabbatar na iya zama ƙasa da na ainihi, saboda ba a bayyana wasu kudaden da aka biya ba.
A cewar rahoton, wani ɓangare na Boko Haram ne ya karɓi kashi 90 cikin 100 na kudin fansar da aka samu a hare-haren garkuwa da mutane a arewa maso gabashin Najeriya.
Sai dai rahoton ya ce arewa maso yammacin ƙasar ce ta fi fuskantar yawan hare-haren garkuwa da mutane da kuma yawan waɗanda aka sace.
SBM ta kiyasta cewa Boko Haram ta samu kusan naira biliyan bakwai, musamman daga wasu manyan hare-hare biyu da aka yi garkuwa da mutane sama da 300 a kowane hari.
Rahoton ya fito ne yayin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin a ceto daruruwan fararen hula da aka yi garkuwa da su a jihar Neja a makon da ya gabata.
Garkuwa da mutane domin neman kudin fansa na ci gaba da zama ɗaya daga cikin manyan matsalolin tsaro a Najeriya, inda masu garkuwa da mutane ke kai hare-hare makarantu, kauyuka da manyan tituna.
SBM Intelligence ta yi gargadin cewa idan gwamnati ba ta samar da cikakkiyar dabara da za ta rage ribar da ake samu daga wannan laifi tare da magance tushen matsalar ba, garkuwa da mutane na iya zama babbar hanyar samun kuɗin gudanar da ayyukan ƙungiyoyin da ke barazana ga tsaron ƙasar.




