“Duk wanda ya ce zai dawo da tallafin man fetur, yaudarar ’yan Najeriya yake yi” – Yari

0
35

“Duk wanda ya ce zai dawo da tallafin man fetur, yaudarar ’yan Najeriya yake yi” – Yari

Daga Wakiliya

Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen Shugaba Tinubu na jam’iyyar APC, Sanata Abdulaziz Yari, ya ce duk wani ɗan siyasa da ke alkawarin dawo da tallafin man fetur yana yaudarar ’yan Najeriya ne.

Tsohon gwamnan jihar Zamfara ya ce babu tanadin tallafin man fetur a cikin kasafin kuɗin shekarar 2023 da Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta amince da shi kafin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya hau mulki.

Yari ya bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo, inda ya ce:

“Kafin Asiwaju ya zo a 2023, babu tallafin mai a kasafin kuɗin 2023. To ta yaya za a tafiyar da shi? Duk wanda yake yaudarar ’yan Najeriya yana cewa zai dawo da wannan abu, ƙarya yake yi.”

Ya ce tallafin man fetur ya kasance babban nauyi ga gwamnatin Najeriya, yana cin kusan Naira tiriliyan 20 a shekara, tare da cewa babu tabbataccen bayani kan yawan man da ake amfani da shi a ƙasar.

Yari, wanda ya taɓa jagorantar Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya, ya ce gwamnonin sun shafe shekaru suna ƙalubalantar NNPC kan ta bayyana ainihin yawan man da ake amfani da shi a kullum, amma ba su samu cikakken bayani ba.

“Babu wanda zai iya gaya maka ainihin adadin litar man da muke buƙata a rana. Suna ƙirƙirar alkaluman ne su aika, sannan mu biya,” in ji shi.

Ya kuma ce a wasu lokuta an sha bayyana cewa ana biyan tallafin man ne saboda ana safarar man zuwa wasu ƙasashen Yammacin Afirka.

Yadda APC za ta yi kamfen

Dangane da yaƙin neman zaɓen 2027, Yari ya ce APC za ta mayar da hankali ne kan “bayanan gaskiya da alkaluma”, maimakon kiran sunayen abokan hamayya ko habaice-habaice.

Ya ce jam’iyyar za ta gabatar da abubuwan da gwamnatin Shugaba Tinubu ta cimma a fannonin tattalin arziki, samar da ababen more rayuwa da tsaro, tare da bayyana abin da take shirin yi.

Yari ya ƙara da cewa gwamnatin na kashe sama da Naira tiriliyan biyu a kowane wata wajen yaƙi da matsalar tsaro, ciki har da sayen makamai, alburusai da sauran kayan aiki.

A cewarsa, kayan aikin tsaron da ake da su a wasu jihohi a yanzu sun fi abin da aka taɓa samu a dukkan Arewacin Najeriya a baya.

Ya ce APC na ganin Shugaba Bola Ahmed Tinubu shi ne mutumin da ya dace ya ci gaba da jagorantar ƙasar.

“Bola Ahmed Asiwaju yana iya ƙoƙarinsa, kuma mun yi imanin shi ne mutumin da ya dace da wannan aiki a karo na biyu,” in ji Abdulaziz Yari.

Leave a Reply